Magana ta fara tsami: Gwamna ya karyata ‘Yan Sanda, ya soma fasa-kwai a kan mutuwar Gulak

Magana ta fara tsami: Gwamna ya karyata ‘Yan Sanda, ya soma fasa-kwai a kan mutuwar Gulak

- Sanata Hope Uzodinma bai yarda ‘Yan IPOB ne suka bindige Ahmad Gulak ba

- Gwamnan na jihar Imo yace mutuwar Alhaji Gulak ta na da burbushin siyasa

- Uzodinma yake cewa da labarin mutuwar nan ta zo masa, bai iya zuwa coci ba

Jaridar Daily Trust ta ce Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya yi magana game da mutuwar Ahmad Gulak, a ranar Litinin, 31 ga watan Mayu, 2021.

Mai girma gwamna Hope Uzodinma ya yi jawabi yayin da ya tara ‘yan jarida a garin Owerri, jihar Imo.

Gwamnan ya nunawa manema labarai cewa maganar da ake yi na cewa dakarun kungiyar IPOB ne suka bindige Marigayi Ahmad Gulak ba gaskiya ba ne.

KU KARANTA: Wanene Ahmad Gulak?

Sanata Hope Uzodinma ya ce da ya ji labarin wasu miyagu sun bindige tsohon hadimin na Goodluck Jonathan, bai iya fita coci a safiyar wannan ranar ba.

Ya ce: “Alhaji Ahmed Gulak ya zo jihar Imo ne domin yin wani aikin kasa, Ya zo Owerri tare da kwamitin majalisa na yi wa tsarin mulkin kasa garambawul.”

“Saboda saukin kansa, sai ya zabi ya fita shi kadai a boye kamar yadda wani amininsa da suke tare ya fada. Wani ne ya rika bin sa daga otel zuwa filin jirgin sama”

Sanata Hope Uzodinma ya kara da cewa: “Shiyasa kisan shi yake yanayi da ainihin harin siyasa.”

KU KARANTA: Kusa a Gwamnatin Zamfara ya jibdi mutum saboda ya caccaki Gwamna

Magana ta fara tsami: Gwamna ya karyata ‘Yan Sanda, ya soma fasa-kwai a kan mutuwar Gulak
Ahmed Gulak Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

“Mummunan kisan Alhaji Ahmed Gulak a jiya, Lahadi, 30 ga watan Mayu, 2021, a hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Sam Mbakwe, ya yi mani ciwo sosai.”

Uzodinma yake cewa tsohon hadimin shugaban kasar ya yi wata irin mutuwar da bai dace ya yi irinta ba. Gidan talabijin Channels TV ta fitar da wannan rahoto.

“Mutuwarsa tayi mani zafi saboda abokina ne. Na yi shirin zuwa coci sai labarinsa ya zo mani, daga nan ban iya fita ibada ba, mutuwa ba ta taba girgiza ni haka ba.”

A ranar Lahadi ne aka rahoto cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun bindige Ahmed Gulak, wanda ya taba zama mai ba shugaban kasa shawara.

Ana zargin 'yan kungiyar IPOB ne suka yi wannan aika-aika, har ana ikirarin cafke wasu mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel