Jami’in Gwamnati ya lakadawa Matashi duka saboda ya soki Gwamnan Zamfara a Facebook

Jami’in Gwamnati ya lakadawa Matashi duka saboda ya soki Gwamnan Zamfara a Facebook

- Maganganun da Abdulrasheed Yandi ya yi a Facebook sun jefa sa a ruwan zafi

- Shugaban ZAROTA ya ci mutuncin wannan matashi saboda ya soki Gwamnati

- Alhazzai Shinkafi ya yi wa Yandi duka don kurum ya tabo Gwamna a Facebook

A makonnin da suka wuce ne Abdulrasheed Buhari Yandi ya yi magana a kan gwamnatin jihar Zamfara a shafinsa na Facebook, hakan ya jefa shi cikin matsala.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto game da Abdulrasheed Buhari Yandi, wanda wani jami’in gwamnati ya ci wa zarafi saboda ya tabo gwamna Bello Matawalle.

A shafinsa na Abdulrasheed Yandi ya rubuta: “Gaskiya an ba ni kunya da na zo Zamfara, babu wani aikin a zo-a gani da na gani a Gusau da daukacin jihar Zamfara.”

KU KARANTA: Daga daukar shi a mota, ya kashe shi, ya jefar da gawa a jeji

Jami’in Gwamnati ya lakadawa Matashi duka saboda ya soki Gwamnan Zamfara a Facebook
Abdulrasheed Buhari Yandi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yandi wanda ‘dan jam’iyyar PDP ne, ya ce gwamnatin nan ba ta cika duk alkawuranta ba, ya ba Bello Matawalle shawarar ya gyara rawarsa ko su sha kashi a 2023.

Bayan ya yi wannan jawabi a dandalin Facebook sai shugaban hukumar, ZAROTA, Aliyu Alhazzai Shinkafi, ya kira shi a waya lokacin ya yi tafiya zuwa garin Sokoto.

Rahotanni sun ce Aliyu Shinkafi wanda ‘dan a-mutun gwamna Matawalle ne, ya dade ya na neman Yandi, kafin ya samu lambar wayarsa a wajen wasu na-kusa da shi.

Shugaban ZAROTA ya yi wa ‘yanuwan wannan Bawan Allah alkawarin cewa zai kai shi wajen gwamna, amma da suka yi ido-biyu, sai ya yi masa ‘dan-karen duka.

KU KARANTA: Buba Galadima: R-APC ta na nan, kwanan nan za a ji durowarta

A wani bidiyo da Legit.ng Hausa ta samu a Twitter, za a ga Aliyu Shinkafi da kansa ya na cin zarafin Abdulrasheed Yandi a kan titi, kafin ya jefa sa a cikin mota.

Daga nan ya zarce da shi zuwa gidansa, inda ya ajiye shi ya kwana, sai washegari aka tafi nemansa.

A cewar Yandi, ‘yanuwansa sun tuntubi ‘yan sanda wadanda suka taimaka suka ceto shi. Wannan mutum ya ce ba don haka ba, da wani labarin na dabam ake yi.

Bayan nan an ji Aliyu Shinkafi ya na fada wa gwamna Matawalle a wayar salula yadda ya casa wannan mutum mai sukarsa, amma ya musanya wannan sauti da ake ji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel