Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Za Ta Ginawa 'Yan Najeriya Miliyan 1.5 Gidaje

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Za Ta Ginawa 'Yan Najeriya Miliyan 1.5 Gidaje

- Gwamnatin Buhari ba ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na ganin ta kyautata rayuwar ‘yan Najeriya

- Fadar shugaban kasa a ranar Lahadi, 30 ga watan Mayu, ta bayyana cewa ta amince da kashe Naira N200bn a aikin gina kasa

- Laolu Akande, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa tsarin zai amfani akalla ‘yan Najeriya miliyan 1.5

Fadar shugaban kasa ta bayyana kudirin ta na daukar nauyin shirin samar da gidaje na kasa (NSHP) don tallafawa 'yan Najeriya sama da miliyan 1.5.

A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta samo, fadar shugaban ta ce gwamnatin tarayya tare da goyon bayan ma’aikatar kudi ta kammala shirye-shirye tare da Babban Bankin Najeriya don daukar nauyin wannan katafaren aikin.

Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Za Ta Ginawa 'Yan Najeriya Miliyan 1.5 Gidaje
Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Za Ta Ginawa 'Yan Najeriya Miliyan 1.5 Gidaje Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake magana kan aikin, Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya ce manufar ita ce ‘yan kasa su mallaki gidaje masu rahusa ta hanyar jingina da kuma bayar da haya ga zabin mallaka.

KU KARANTA: Sharhin 'Yan Najeriya Game Da Mutuwar Tsohon Hadimin Jonathan, Ahmed Gulak

Akande ya kara da cewa ana sa ran shirin zai kuma samar da ayyukan yi ga kasa da 'yan kasa miliyan 1.8.

Har ila yau, fadar shugaban kasar ta ce shirin tattalin arziki mai dorewa (ESP) na Solar Power Naija, ya yi niyyar samar da wutar lantarki ne ga gidaje miliyan biyar da zai wadaci 'yan Najeriya sama da miliyan 25 a yankunan karkara da birane a fadin kasar.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai ya ce:

"Daya daga cikin kamfanonin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana dake aiwatar da shirin ESP Solar Power Naija, A-SOLAR, zai isar da unit sama da 100,000 a duk fadin kasar a zangon farko na aikin, ya kuma samu wani karin ci gaba, tare da kammala fitar da kudade daga Babban Bankin Najeriya (CBN)."

KU KARANTA: Ba Zaku Tsira Ba, Sai Na Hukunta Ku: Buhari Ga Wadanda Suka Kashe Ahmed Gulak

A wani labarin, Aranar Asabar 29 ga Mayu, 2021 Shugaba Buhari ke cika shekaru biyu a wa’adin mulkinsa na biyu, a hade shekaru shida bayan hawansa mulki a 2015.

Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaba Buhari da ya yi amfani da jawabinsa na ranar wajen amsa wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta gaza, sabanin jawabansa na baya da ta ce suke ikirarin samun nasarorin bogi.

Sakataren yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki bisa zargin neman yi wa ’yan Najeriya ikirarin samun nasarori na bogi, alhali babu wata nasarar azo-a-gani da gwamnatin APC ta yi ko ta kammala a tsawon shekaru shida da take mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.