Wata Sabuwa: An Zargi Obasanjo da Shirya Makarkashiyar Kifar Da Gwamnatin Buhari

Wata Sabuwa: An Zargi Obasanjo da Shirya Makarkashiyar Kifar Da Gwamnatin Buhari

- Wata kungiyar magoya bayan Buhari ta zargi tsohon shugaban kasa Obasanjo da shiryawa Buhari makarkashiya

- Kungiyar ta ce tsohon shugaban ya hada kan wasu fitattun mutane a Najeriya don kifar da gwamnatin Buhari

- Sai dai, kungiyar ba ta ambaci sunan tsohon shugaban kasar ba kai tsaye, lamarin da ya jawo ake zargin Obasanjo

Kungiyar 'Buhari Media Organisation (BMO)' ta zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da shirya makarkashiyar tumbuke Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa a ranar Lahadi, kungiyar ta ce wani "tsohon shugaban farar hula" da "gungun" wasu "makirai" ne suke kitsa wannan mummunan makircin, PM News ta ruwaito.

Ta ce masu shirya makarkashiyar da sunan ‘fitattun mutane’ sun shirya tayar da zaune tsaye don tilasta wa Shugaba Muhammadu Buhari sauka.

Ko da yake kungiyar ta nisanci yin ishara kai tsaye zuwa ga Obasanjo, amma babu shakka akwai tunanin Obasanjo take nufi.

KU KARANTA: Labari Mai Dadi: Gwamnatin Buhari Za Ta Ginawa 'Yan Najeriya Miliyan 1.5 Gidaje

Wata Sabuwa: An Zargi Obasanjo da Shiryawa Buhari Makarkashiyar Kifar Da Gwamnatinsa
Wata Sabuwa: An Zargi Obasanjo da Shiryawa Buhari Makarkashiyar Kifar Da Gwamnatinsa Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

BMO ta gargadi tsohon shugaban da abokan tafiyarsa da su hanzarta kawar da tunanin da kuma tseratar da kasar daga rikicin tsarin mulki da rikice-rikicen cikin gida.

Kungiyar ta magoya bayan Buhari ta yi kira ga 'yan Najeriya da su yi taka tsantsan da makiricin "fitattun mutane masu karfin iko da a shirye suke su jefa kasar cikin wani mummunan rikici da zai ci gaba da kasancewa."

Obasanjo, daya daga cikin shugabannin farar hula biyu da ke raye, shi ne kadai zai iya tara ‘fitattun mutane’ don yin suka a kan shugabancin Buhari.

A cikin shekarar 2018, Obasanjo ya yi kokari ya hada kan 'yan siyasa don lalata sake zaben Buhari. Amma shirin ya faskara.

Sai dai, ICIR ta lura cewa tsoffin shugabannin farar hula guda biyu a Najeriya sune Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Obasanjo ya kasance shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007, yayin da Jonathan ya kasance a matsayin shugaba daga shekarar 2010 zuwa 2015.

Buhari ya karbi mulki ne daga hannun Jonathan bayan shan kaye a zaben shugaban kasa a shekarar 2015.

Duk da cewa gwamnatin Buhari ta ci gaba da dora laifin kalubalen kasar a kan gwamnatin Jonathan, da alama shugabannin biyu suna da kyakkyawar alakar abokantaka.

A ranar 28 ga Mayu, Jonathan ya gana da Buhari a Fadar Shugaban Kasa kan rikicin siyasa a Mali. Jonathan bai fito fili ya soki Buhari ba, duk da cewa dukkansu suna cikin jam’iyyun siyasa masu karo da juna.

A gefe guda kuma, ana iya bayyana Buhari da Obasanjo a matsayin abokan gaban siyasa.

KU KARANTA: Jonathan Ya Yi Jimamin Mutuwar Ahmed Gulak, Ya Yi Martani Game Dashi

A wani labarin, Obasanjo, daya daga cikin shugabannin farar hula biyu da ke raye, shi ne kadai zai iya tara ‘fitattun mutane’ don yin suka a kan shugabancin Buhari.

A cikin shekarar 2018, Obasanjo ya yi kokari ya hada kan siyasa don lalata sake zaben Buhari. Amma shirin ya faskara.

Sakataren yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki bisa zargin neman yi wa ’yan Najeriya ikirarin samun nasarori na bogi, alhali babu wata nasarar azo-a-gani da gwamnatin APC ta yi ko ta kammala a tsawon shekaru shida da take mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.