Gwamnan Neja Ya Shilla Ƙasar Waje Tare da Matarsa Bayan Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Islamiyya a Jiharsa

Gwamnan Neja Ya Shilla Ƙasar Waje Tare da Matarsa Bayan Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Islamiyya a Jiharsa

- Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya shilla ƙasar waje tare da mai ɗakinsa awanni ƙadan da sace ɗalibai a jiharsa

- Rahotanni sun bayyana cewa a jiya ne wasu yan bindiga suka sace ɗaliban islamiyya sama da 200 a garin Tegina

- Gwamnan ya tabbatar wa da iyayen yaran cewa yayan su zasu dawo gida cikin ƙoshin lafiya

Awanni kaɗan bayan sace ɗaliban islamiyya da ba'a san adadin su ba a Tegina ƙaramar hukumar Rafi, Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello, ya tafi ƙasar waje, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Gano Yan Bindigan da Suka Kashe Ahmed Gulak, Ta Sheƙe Wasu

Legit.ng hausa ta gano cewa gwamna Abubakar sani ya tafi ƙasar wajen ne tare da mai ɗakinsa.

A wani jawabi da sakataren yaɗa labarai na jihar, Mary Noel Berje, ya fitar, yace gwamnan yayi wannan tafiya ne domin nemo hanyoyin da za'a warware matsalolin tsaron da suka addabi jihar.

Gwamnan Neja Ya Shilla Ƙasar Waje Tare da Matarsa Bayan Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Islamiyya a Jiharsa
Gwamnan Neja Ya Shilla Ƙasar Waje Tare da Matarsa Bayan Yan Bindiga Sun Sace Ɗaliban Islamiyya a Jiharsa Hoto: @Abusabello
Asali: Twitter

Wani sashin jawabin yace: "Gwamnan, wanda muke tsammanin dawowarsa cikin ƙanƙanin lokaci, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa zata kuɓutar da ɗaliban, zasu dawo gida lami lafiya."

"Gwamnan Abubakar Sani ya ƙara jaddada wa al'ummar jiharsa cewa gwamnatinsa zata yi duk me yuwuwa domin kare lafiya da dukiyoyin mutanen ta, kuma ya tabbatar da cewa za'a cigaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Neja."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa a Ibadan

"Gwamnan ya kuma tabbatar wa iyayen yaran da aka sace cewa 'yayan su zasu dawo gida cikin ƙoshin lafiya, yayin da aka baiwa hukumomin tsaro umarnin suyi duk me yuwuwa domin kuɓutar da ɗaliban."

Gwamnan ya kuma roƙi mazauna jihar da su taimaka wa jami'an tsaro da sahihan bayanai domin ganin an kuɓutar da ɗaliban cikin gaggawa.

A kalla dalibai 200 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai garin Tegina a karamar hukumar Rafi na jihar Niger, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

A wani labarin kuma Ahmed Gulak Ya Fita Masaukinsa Ba Tare da Sanin Mu Ba, Yan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske

Rundunar yan sandan jihar Imo, ta bayyana cewa marigayi Ahmed Gulak ya fita daga masaukinsa zuwa filin jirgi ba tare da sanin yan sanda ba.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka halaka hadimin na Jonathan a Owerri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel