Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda aka saci mutane rututu a kauyen Neja da rana-tsaka

Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda aka saci mutane rututu a kauyen Neja da rana-tsaka

- Shehu Sani ya ce ya samu labarin shigowar ‘Yan bindiga garin Tegina jiya

- Tsohon Sanatan yake cewa ‘Yan bindigan sun shiga kauyen ne kan babura

- Miyagun suna rike da makamai, daga nan suka arce da mutane zuwa Jeji

A ranar Lahadin nan, tsohon Sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani, ya yi magana game da satar mutane da aka yi a karamar hukumar Tegina, jihar Neja.

Sanata Shehu Sani ya na cikin wadanda suka fara fadakar da jama’a cewa ‘yan bindiga sun shiga wani kauye da ke garin Tegina, sun yi gaba da mutane.

Da yake magana a shafin Twitter, Shehu Sani ya bayyana cewa an fada masa yadda wadannan miyagun ‘yan bindiga suka duro kauyen a bisa baburansu.

KU KARANTA: An fito da wasu daga cikin wadanda aka sace a Neja

Shehu Sani wanda ya wakilci mutanen Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce ‘yan bindigan sun zo dauke da miyagun makamai, suka yi gaba da mutane.

A lokacin da Sanata Sani yake magana, har aikin gama ya gama, domin an yi garkuwa da mutanen kauyen, har wadanda suka boye sun soma fito wa.

Kwamred Sani ya rubuta: “Wani mai garin kauye ya yi magana da ni mintuna 30 da suka wuce, ya ce mani ‘yan bindiga sun auka wa kauyen Tegina, a Neja.”

Da kimanin karfe 5:00 na yamma, ya ce: “Sun zo a kan babura dauke da manyan makamai, suka yi awon-gaba da mutane da yawa, suka shiga da su cikin jeji.”

Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda aka saci mutane rututu a kauyen Neja da rana-tsaka
Sanata Shehu Sani Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: An gano wadanda suka kashe Gulak a Imo

“Mafi yawan mutanen garin da suka sulale, suna fitowa daga cikin wuraren da suka boye.

Ganin yadda ‘yan bindigan suka fitini yankin Arewa, ‘dan siyasar ya ce lokaci ya yi da za a bankado wadanda suke yin wannan ta’adi, domin a hukunta su.

Duk a jiyan, fitaccen ‘dan siyasar ya bada labarin kashe Ahmad Gulak a jihar Imo, sannan ya ce an sace wani ‘dan majalisar Nasarawa a hanyar Kaduna-Akwanga.

A makon jiya kun ji cewa Abubakar Shekau ya fallasa yadda 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka rika samun miliyoyin kudi da makamai daga kasashen waje.

A wani faifai, an ji Abubakar Shekau ya na cewa Boko Haram ta yi wa manyan kungiyoyin ta’addan Duniya mubaya’a a lokacinsa, don haka suka samu agaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel