Bahaushen Da Ya Riƙe Amanan Bayarabe Tsawon Shekaru 30 Ya Sha Yabo

Bahaushen Da Ya Riƙe Amanan Bayarabe Tsawon Shekaru 30 Ya Sha Yabo

- Wani dattijo ya nuna riƙon amana a yayin da ya kula da gonar da tsohon mai gidansa ya rasu ya bari tsawon shekaru ba tare da ana biyansa albashi ba

- Shekaru kimanin 30 bayan rasuwar mai gidansa, dattijon yana son ya koma garinsu hakan yasa ya bayyana abin alherin da ya aikata

- Ɗan tsohon mai gidan dattijon da a yanzu ya girma ya ce bai san yadda zai gode masa ba

Wani matashi ɗan Nigeria mai suna @sarnchos a ranar Talata, 25 ga watan Mayu ya bayyana yadda wani dattijon bahaushe ya riƙe amanan mahaifinsa tsawon shekaru 30.

A wani rubutu da ya yi a baya tun shekarar 2019, ya rubuta kan yadda wani mutum da ya fi shekaru 90 a lokacin ya riƙa kula da gonar mahaifinsa tun a 1992.

Rikon Amana: Yadda Bahaushe ya tsare gadon Bayarabe na tsawon shekaru 30
Rikon Amana: Yadda Bahaushe ya tsare gadon Bayarabe na tsawon shekaru 30. @sarnchos
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Samamen Da Sojoji Suka Kai Mabuyar Ƴan Aiken Ƴan Boko Haram

@sarnchos ya bayyana cewa tsawon shekaru kimanin 30, dattijon bai taɓa karbar wani albashi ko lada ba sai dai yana ciyar da kansa ne da abin da ya ke noma wa a gonar.

Matashin, wanda ya yi matukar farin cikin irin wannan riƙon amana da gaskiya ya ce bai san yadda zai saka wa dattijon ba.

A shekarar 2021, matashin ya yi nuni da rubutun da ya yi a 2019 ya kuma ce dattijon na son komawa garinsu a jihar Kano.

Baba, kamar yadda ake kiransa, ya shaidawa @sarnchos cewa ya cika alƙawarin da ya ɗauka na kulawa da filin da aka ba shi amana.

Don hakan yana son ya koma gida.

Zai koma garinsu mai suna Babeji a jihar Kano (garinsu hamshaƙin attajirin dan kasuwa Dangote).

Ya tsufa sosai don haka yana son ya koma gida ya ƙarasa sauran rayuwarsa.

KU KARANTA: An Yi Gumurzu Tsakanin Sojoji Da Mayaƙan Boko Haram a Diffa

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin sharhin da mutane suka yi game da labarin

@LocaleMann ya ce:

"Don Allah ka yi ƙoƙari ka saka yaronsa ko yaransa makaranta a matsayin don tunawa da abin da Baba ya maka."

@okbabalola ya ce:

"Don Allah ka saka shi a jirgin sama - Kana ganin yana da lafiyar da zai iya shiga motar haya zuwa garinsu? Ka saka shi a jirgi har gida ku tafi kaga garinsu."

@yumlat ta ce:

"Na kusan zubar da hawaye yayin da na ke karanta wannan labarin ina matukar son mutane masu rikon amana kuma abin yana birge ni. Allah ya saka wa Baba da alheri, rabuwa da wahala ya ke."

A wani labarin daban, Mahukunta a Makarantar Sakandare ta Mata na St Claire's Girls Grammar School, Offa, jihar Kwara sun rufe makarantar saboda firgici kan jin wasu muryoyi da ake zargin 'iskokai' ne a makarantar, The Nation ta ruwaito.

Bayannan da aka tattaro sun nuna cewa mahukunta a makarantar sun umurci iyaye da masu kula da yara su tafi da yaransu gidajensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel