Matana Sun Gujeni Dana Kamu da COVID-19, Saura a Samu COVID-25 a Gaba, El-Rufa’i

Matana Sun Gujeni Dana Kamu da COVID-19, Saura a Samu COVID-25 a Gaba, El-Rufa’i

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana yadda ya kawo COVID-19 jihar Kaduna daga wani gwamna

- Ya ce matansa sun gujeshi lokacin da ya kamu da cutar COVID-19 a shekar da ta gabata ta 2020

- A cewarsa, watakila nan gaba a sake samun wata cutar ko dai COVI-25 ko 30 saboda wasu dalilai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Asabar ya tuna yadda wani gwamna ya shafa masa cutar COVID-19 shekarar 2020, jaridar Punch ta ruwaito.

El-Rufai, yayin da yake jawabi a laccar Ahmadu Bello Foundation ta bakwai a Kaduna ranar Asabar, ya kuma ce akalla mutane 50,000 ne cutar za ta kashe a shekarar da ta gabata idan da ba a sanya takunkumi ba.

Gwamnan, a ranar 26 ga Maris, 2020, ya sanya takunkumi a jihar Kaduna, bayan barkewar cutar COVID-19 ya kuma dage dokar a ranar 9 ga Yunin, 2020, bayan kwanaki 75.

KU KARANTA: Kungiyar Kiristoci Ga Sanataoci: Ba Ruwanmu Da Addini a Najeriya Balle Shari'a

Matana Sun Gujeni Dana Kamu da COVID-19, Saura a Samu COVID-25 a Gaba, El-Rufa’i
Matana Sun Gujeni Dana Kamu da COVID-19, Saura a Samu COVID-25 a Gaba, El-Rufa’i Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewarsa, ya kwashe kwanaki 26 a kebe, ya kara da cewa hatta matansa sun guje shi a lokacin.

El-Rufai ya ce, “Wani gwamna ne ya shafa min COVID-19ni kuma na kawo ta Kaduna. An kulle ni tsawon kwanaki 26. Matana sun guje ni.

"Da mutane dubu hamsin a Kaduna za su mutu saboda COVID-19a shekarar da ta gabata, amma Jihar Kaduna ce ta fara sanya dokar kulle.

“Ina mai farin cikin cewa saboda COVID-19 mun samu damar samar da wuraren kwantar da masu cututtuka masu harbuwa a asibitocinmu.

"Mutane suna tafiya a fadin duniya don haka akwai yiwuwar samuwar 'COVID-25' ko 30. Tare da abin da ke faruwa a Indiya, yanayin yana da ban tsoro. Amma Allah ya tausaya mana.”

Gwamna Nasir El-Rufai ya yi gargadin cewa duk da cewa yawan kamuwa da cutar ta COVID-19 ya ragu sosai, amma za a samu karin cututtukan a nan gaba saboda lamarin ya zama ruwan dare game duniya, in ji jaridar Vanguard.

KU KARANTA: Cika Shekara 6: Banda Karya, Ka Amsa Cewa Ka Gaza Kawai, PDP Ta Roki Buhari

A wani labarin, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar na cikin aminci a hannun shugaba Buhari duk da kalubalen tsaro da ta ke fuskanta, The Punch ta ruwaito.

Ya shawarci ‘yan kasa da kada su yarda da mummunan hasashe game da Najeriya saboda ba za su zo ba.

Ministan ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye da mukarrabansa a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel