'Yan bindiga sun saka hedkwatar jami'an hukumar shige da fice bam a Abia

'Yan bindiga sun saka hedkwatar jami'an hukumar shige da fice bam a Abia

- 'Miyagun 'yan bindiga sun kai mugun farmaki hedkwatar kula da shige da fice dake jihar Abia

- An gano cewa sun saka bam ne inda suka tashe shi sannan suka bi ababen hawa suka kone

- Daga nan suka budewa jami'an hukumar wuta, lamarin da ya kawo mutuwar wasu daga ciki

'Yan bindiga wadanda ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne sun kai mugun hari hedkwatar hukumar kula da shige da fice ta Najeriya dake Ubakala, karamar hukumar Umuahia ta kudu a jihar Anambra.

Hedkwatar hukumar bata da tazara da inda 'yan sanda suke wadanda aka kaiwa hari tun farko a Ubakala kuma hakan ya kawo mutuwar jami'an 'yan sandan biyu, Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa sun sakawa hukumar NIS bam inda ya tashi da ita sannan suka budewa jami'an dake aiki wuta, lamarin da ya kawo ajalin wasu daga ciki.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya bayyana Basheer Mohammed a matsayin shugaban hukumar NAPTIP

'Yan bindiga sun saka hedkwatar jami'an hukumar shige da fice bam, sun sheke wasu jami'an
'Yan bindiga sun saka hedkwatar jami'an hukumar shige da fice bam, sun sheke wasu jami'an. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da yawon jirgin sama ranar zagayowar haihuwarta

Daily Trust ta tabbatar da yadda wasu ababen hawa dake farfajiyar wurin aka banka musu wuta kuma suka kone kurmus.

Har ila yau, sashin bincike na musamman na hukumar 'yan sandan Najeriya an kai masa hari a ranar Asabar da safe, Premium Times ta ruwaito.

'Yan bindigan da suka kai 50 ne suka kai harin inda suka bayyana rabinsu tsirara. An ga wasu daga ciki sun sagale zakaru masu rai a wuyansu yayin da wasu daga cikinsu ke rike da bindiga kirar AK 47.

Sun kai farmaki wurin 'yan sandan inda suka bankawa ofishin wuta.

Duk kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Geoffrey Ogbonna, ya gagara saboda bai dauka wayarsa ba da aka dinga kira.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a 2020 zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022.

Wannan na kunshe ne a wata wallafa da gwamnatin Najeriya tayi a shafinta na Twitter a ranar Laraba 26 ga watan Mayun 2021.

Wani bangare na wallafar yace: "Sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng