Labari mai dadi: FG ta bayyana lokacin da karin albashin malaman makaranta zai fara aiki

Labari mai dadi: FG ta bayyana lokacin da karin albashin malaman makaranta zai fara aiki

- Sabon tsarin albashi na musamman na malaman makaranta da Shugaba Buhari ya amince dashi zai fara aiki a watan Janairun 2022

- Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan a wallafar da tayi a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 26 ga watan Mayun 2021

- Shugaban kasan yace an yi haka ne domin karfafawa malaman makaranta guiwa ta yadda zasu koyar da ilimi mai inganci

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a 2020 zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022.

Wannan na kunshe ne a wata wallafa da gwamnatin Najeriya tayi a shafinta na Twitter a ranar Laraba 26 ga watan Mayun 2021.

KU KARANTA: Matasa sun kone mahaukaciya bayan kama ta da suka yi da makamai a Legas

Labari mai dadi: FG ta bayyana lokacin da karin albashin malaman makaranta zai fara aiki
Labari mai dadi: FG ta bayyana lokacin da karin albashin malaman makaranta zai fara aiki. Hoto daga @NGRPresident
Asali: UGC

Wani bangare na wallafar yace: "Sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022."

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabon albashi na musamman ga malaman makaranta a ranar malaman makaranta ta duniya wacce ta fada a Litinin, 5 ga watan Oktoban 2020.

Kamar yadda Adamu Adamu, ministan ilimi ya sanar, an gabatar da sabon albashin ne domin karfafawa malaman makaranta guiwa.

Babu tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta tuntubi gwamnonin jihohi kafin sanar da sabon albashin ganin cewa wasu daga cikinsu sun soki hakan.

A wani rahoto da The Nation ta ruwaito a wancan lokacin, tace gwamnonin Najeriya basu ji dadin sabon albashin ba.

An tattaro cewa gwamnonin sun tabbatar da cewa malaman makaranta dake aiki da gwamnatin tarayya ne kadai zasu more wannan garabasar da shugaban kasar ya sanar.

KU KARANTA: Rikicin shugabanci: ISWAP sun kama kwamandojin Shekau, sun gana da wadanda suka yi mabaya'a

A wani labari na daban, jami'an 'yan sanda da kungiyar 'yan sa kai dake Hayin Daudu a garin Gusau na jihar Zamfara sun halaka 'yan bindiga 10 a ranar Litinin.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya sanar da cewa 'yan sanda da 'yan sa kai sun gaggauta zuwa inda aka kira su sakamakon harin da 'yan bindigan ke kaiwa Hayin Daudu, Premium Times ta ruwaito.

"'Yan sandan da aka tura yankin Mada, sun hadu da wata kungiyar sa kai wurin karfe 11 na dare inda suka yi gaggawar zuwa Kauyen Hayin Daudu sakamakon kiran gaggawa da suka samu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel