Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da yawon jirgin sama ranar zagayowar haihuwarta

Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da yawon jirgin sama ranar zagayowar haihuwarta

- Wani magidanci ma'abocin soyayya ya kwashe matarsa tare da iyalinsa gaba daya inda ya kaisu hutu wani gari domin zagayowar ranar haihuwarta

- Bai tsaya a nan ba, ya gwangwaje matarsa da tafka-tafkan motoci biyu, kirar Lamborghini da kuma Rolls Royce

- Matar mai suna Mary ta cika da farin ciki da yadda ranar zagayowar haihuwarta ta kasance inda tace burikanta sun gama cika

Wani miji ma'abocin soyayya ya baiwa matarsa kyauta wacce za a iya cewa mafi shaharar kyauta da za a iya baiwa mutum a shekarar 2021.

Wani dan kasar Amurka mai amfani da suna @MrZothegoat ya baiwa matarsa mai suna Mary Skittlez matukar mamaki a ranar zagayowar haihuwarta wanda ya hada da motocin alfarma biyu.

Dukkan shagalin da ta shiga a ranar zagayowar haihuwarta an nadesu a bidiyo inda ta wallafa a shafinta na Instagram wanda ya hada tun daga shigarsu jirgi har zuwa kammala shagalin.

KU KARANTA: Da duminsa: Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi

Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da jirgi 1 a ranar zagayowar haihuwarta
Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da jirgi 1 a ranar zagayowar haihuwarta. Hoto daga @mrzothegoat
Asali: Instagram

KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara

Abu na farko da magidancin ya fara shine tattara iyalansa a jirgin sama na yawo, matar tana shiga aka fara mata ihu tare da murna, daga nan ne ta gane cewa duk da 'ya'yanta na ciki.

A lokacin da suka isa inda suke so, Mary ta fito inda ta ci karo da mota kalar bula kirar Lamborghini SUV wacce aka ajiye.

Cike da farin ciki Mary ta fada motar tare da shigewa wurin mazaunin direba, ashe ba a nan aka tsaya ba.

Daga nan aka yi mata jagora zuwa wani wuri inda aka fara liyafa. Bayan cire mata kyallen da aka rufe mata ido, ta ga dukkan 'yan uwanta da suka hada da mahaifinta wanda ya yi doguwar tafiya domin samun shagalin.

Bayan dare yayi kuma duk sun gaji tare da fitowa domin zuwa masauki, mijinta ya jagoranci Mary zuwa inda wata mota kirar Rolls Royce take a matsayin kyauta ta biyu.

A wani labari na daban, matashi dan Najeriya mai shekaru 23 mai suna Adam Dalla ya aura fitacciyar 'yar siyasa a Adamawa mai suna Barista Jamila Babuba.

Kamar yadda wallafar da shafin @lindaikejiblogofficial yayi a Instagram, ma'auratan sun angwance a ranar 18 ga watan Mayun 2021 kuma zasu yi walimar aurensu ne a ranar 31 ga watan Mayun 2021.

Kyawawan hotuna da katin gayyatar liyafar bikin sun bazu a kafafen sada zumunta kuma jama'a sun matukar nuna sha'awarsu da wannan soyayya dake tsakanin ma'auratan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel