Da duminsa: Buhari ya bayyana Basheer Mohammed a matsayin shugaban hukumar NAPTIP

Da duminsa: Buhari ya bayyana Basheer Mohammed a matsayin shugaban hukumar NAPTIP

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Basheer Mohammed a matsayin sabon shugaban hukumar NAPTIP

- Har ila yau, zasu yi musayar hukuma ne da Imaan Sulaiman Ibrahim wacce ke shugabantar NAPTIP inda zata koma NCFRMI

- Shugaban kasan yace an yi hakan ne domin samun ingancin aiki a karkashin ma'aikatar jin kai da walwalar 'yan kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Basheer Mohammed a matsayin sabon darakta janar na hukumar yaki tare da hana safarar mutane (NAPTIP).

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.

Shehu yace shugaban kasan ya amince da wasu manyan sauye-sauye a ma'aikatar tallafi da jin kai tare da walwalar 'yan kasa.

Shehu yace an dauka wannan matakin ne domin a samar da burin gwamnati na tabbatar da aiki mai kyau a cikin hukumomin biyu.

KU KARANTA: Dakarun sojin Najeriya sun damke masu samarwa Boko Haram man fetur a Yobe

Da duminsa: Buhari ya bayyana Basheer Mohammed a matsayin shugaban hukumar NAPTIP
Da duminsa: Buhari ya bayyana Basheer Mohammed a matsayin shugaban hukumar NAPTIP. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi

Takardar tace Imaan Sulaiman Ibrahim wacce har yanzu take shugaban hukumar NAPTIP za ta mika ragamar hukumar zuwa hannun Basheer Mohammed kwamishinan tarayya na hukumar 'yan gudun hijira inda ita kuma za ta karba ragamar hukumar da ya baro.

Shehu ya kara da cewa shugaban kasa ya kara bada umarnin sauyin ya fara aiki bayan shirya komai na mika ragamar hukumomin.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a 2020 zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022.

Wannan na kunshe ne a wata wallafa da gwamnatin Najeriya tayi a shafinta na Twitter a ranar Laraba 26 ga watan Mayun 2021.

Wani bangare na wallafar yace: "Sabon albashi na musamman na malaman makaranta wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairun 2022."

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito muku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sabon albashi na musamman ga malaman makaranta a ranar malaman makaranta ta duniya wacce ta fada a Litinin, 5 ga watan Oktoban 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel