Wani ƙusa a APC ya fadawa hadimin Shugaban kasa, Garba Shehu, ya iya bakinsa

Wani ƙusa a APC ya fadawa hadimin Shugaban kasa, Garba Shehu, ya iya bakinsa

- Cif Olusegun Osoba ya soki aikin Garba Shehu da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC

- Tsohon Gwamnan yace hadimin shugaban kasar ya rika auna kalamansa

- ‘Dan siyasar ya zargi ‘Yan APC da rashin hadin-kai a kan sha’anin kasa

A ranar Laraba, 28 ga watan Mayu, 2021, tsohon gwamnan jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, ya caccaki hadimin shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Olusegun Osoba ya ja-kunnen mai magana a madadin shugaban Najeriyar ya bi sannu a hankali ka da jawabinsa ya rika sha ban-bam da na mai gidansa.

Jagoran na APC ya gargadi Garba Shehu a kan yin kalaman da suka bambanta da ra’ayin mai girma Muhammadu Buhari da matsayar jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ceto Shugabannin Mali

Jaridar Punch ta ce jigon na jam’iyyar APC mai mulki a kudu maso yammacin Najeriya ya yi wannan bayani ne da aka yi hira da shi a tashar Arise TV.

Rahoton ya ce Segun Osoba ya maida martani ga Garba Shehu na adawar da ya nuna a kan matsayar gwamnonin Kudu na haramta kiwon dabbobi a fili.

Osoba ya kuma yi tir da yadda ‘ya ‘yan jam’iyyarsu ta APC ba su magana da yawu daya a kan rikicin makiyaya da manoma da ya addabi jihohin kasar nan.

“Gwamnonin nan ‘yan APC ne, kuma Garba Shehu tsohon shugaban kungiyar editocin Najeriya ne, kuma kwararren wanda ya san aiki.” Inji tsohon gwamnan.

Wani kusa a APC ya fadawa babban hadimin Shugaban kasa, Garba Shehu, ya iya bakinsa
Osoba ya ja-kunnen Garba Shehu Hoto: @Olumide_Osoba
Asali: Facebook

KU KARANTA: Bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya da jihohi bashi ya tashi da 170%

“Ina ba shi shawarar ya koma kan aikinsa, ya auna abin da yake fada, ya yi hattara da yadda yake tsoma baki. Gwamnati guda ce, amma muna yi wa kanmu adawa.”

“Tun farko, gwamnatin tarayya ba ta da wani fili a Najeriya, face na birnin tarayya. Tsarin mulki ya ce gwamnonin jihohi ne suke da iko da filayen da suke iko."

‘Dan siyasar ya ankarar da gwamnati, ya ce ba dole ba ne a tsarin tarayya, kowa ya samu yadda yake so.

A makon nan aka ji Injiniya Buba Galadima, wanda tsohon-na-kusa da shugaba Muhammadu Buhari ne, ya na cewa babu ruwansa da jam'iyyun APC da PDP.

Buba Galadima ya bayyana cewa shi fa ba ‘dan jam’iyyar PDP ba ne, kamar yadda ake tunani, ya ce har gobe shi yana tare da r-APC da ta bangare daga cikin APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng