Da duminsa: Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi

Da duminsa: Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi

- Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinjoji 160 ya kife a kogin Neja yayin da ya nufi jihar Kebbi

- Kamar yadda jami'ai suka sanar, jirgin mutum 80 zai iya dauka amma aka lafta fasinjojin

- Masu taimakon gaggawa sun ceto mutum 22 amma kusan mutum 140 babu ko duriyarsu

Fasinjoji masu tarin yawa sun nitse a yankin arewa maso yammacin Najeriya a ranar Laraba bayan tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Neja, jami'i mazaunin yankin ya tabbatar.

Jirgin ruwa da ya bar jihar Kebbi yana tunkarar yankin arewa maso yammacin jihar Kebbi ya fashe sannan ya nitse, Abdullahi Buhari Wara, hakimin Ngaski ya tabbatar.

"Tuni dai masu ceto suka fada kogin amma mutum 22 tare da gawar mutum daya suka iya tsamowa," Wara yace a yanzu kusan fasinjoji 140 ne babu duriyarsu.

KU KARANTA: Jaja Wachuku: Jakadan Najeriya na farko da ya fara yaki da babancin launin fata a UN

Da duminsa: Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi
Da duminsa: Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi
Asali: Original

Wara ya dora laifin hatsarin ga wadanda suka tafkawa jirgin ruwan kaya domin kuwa bai wuce ya dauka fasinjoji 80 ba, Daily Trust ta ruwaito.

An kara da zubawa jirgin ruwan buhunan kasan da aka debo daga wurin hakar zinari, jami'in yace.

A farkon watan nan ne kusan mutum 30 ruwa ya tafi dasu bayan sun dankarawa jirgin ruwa kaya a tsakiyar jihar Neja.

Jirgin ruwan dake dauke da 'yan kasuwa 100 ya rabe biyu bayan ya ci karo da wani abu yayin da guguwa ta tashi suna dawowa daga kasuwa, kamar yadda jami'an hukumar taimakon gaggawa suka sanar.

KU KARANTA: Jigawa: 'Yan sanda sun damke mutum 5 akan zargin lakadawa shugaban APC duka

A wani labari na daban, fusatattun jama'a sun bankawa wata mahaukaciya wuta a yankin Abule Ado dake jihar Legas a ranar Litinin, 'yan sanda suka tabbatar.

Matar da aka kone an kama ta da jaririyar sata da kuma bindiga kirar AK 47 guda uku kafin a kasheta, Premium Times ta ruwaito.

Amma 'yan sanda sun kwatanta lamarin da kisan kai tare da daukan hukunci a hannu domin ba a samu jaririyar ko makaman daga mahaukaciyar ba.

Muyiwa Adejobi, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Legas a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, yace sun fara bincike a kan lamarin da zummar cafke wadanda ake zargi da kisan kan, The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: