Sabbin jiragen yaki, Super Tucano, guda 6 zasu iso a watan Yuli, Fadar shugaban kasa

Sabbin jiragen yaki, Super Tucano, guda 6 zasu iso a watan Yuli, Fadar shugaban kasa

- Yan ta'addan Boko Haram da yan bindiga sun shiga uku, an kusa kawowa Najeriya jiragen yaki

- An kammala kera jiragen a kasar Amurka kuma ana yiwa jami'an Sojin Najeriya horo

- Jiragen Super Tucano 12 Najeriya ta biya kudinsu a shekarar 2018

Fadar shugaban kasa, a ranar Alhamis, ta ce shida cikin sabbin jiragen yaki 12 da gwamnati tayi oda daga kasar Amurka za su iso a watan yuli, 2021.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki mai taken 'Jiragen Super Tucanon Najeriya zasu iso tsakiyar watan Yuli 2021.'

Yace: "Shida cikin jiragen Super Tucano 12 na kan hanyar zuwa tsakiyar Yuli 2021. Akwai matukan jirgin Najeriya 14 dake horo a Moody Air Force Base dake Georgia."

A watan Febrairun 2018, gwamnatin tarayya ta yi odan jiragen SuperTucano 12 a farashin $496million.

KU KARANTA: Ba Wanda Ya Canza Maka Kalamanka Kan Kudin Makamai, Gwamna Wike Ga NSA Monguno

Sabbin jiragen yaki, Super Tucano, guda 6 zasu iso a watan Yuli, Fadar shugaban kasa
Sabbin jiragen yaki, Super Tucano, guda 6 zasu iso a watan Yuli, Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa

A bangare guda, mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma'a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su. Y

a bayyana hakan ne yayin tsokaci kan kalaman mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel