Riƙon alƙawari: Tsawon shekaru 30 Bahaushe na kula da dukiyar Bayarabe, ya damƙata ga magada
- Wani tsoho ya nuna karfin amana yayin da ya kula da dukiyar maigidansa shekaru da yawa bayan mutuwarsa ba tare da karbar albashi ba
- Shekaru da dama bayan rasuwar maigidan nasa, tsohon ya yi ritaya kuma zai koma mahaifarsa, yana mai bayyana cewa ya kammala dukka aikinsa
- Dan mai dukiyar ya ce bai san yadda zai saka wa mutumin da ya nuna musu matukar biyayya ba
Wani labari da ya rusa bangon ƙabilanci ya bayyana kuma hakan ya bayar da burin samun makoma mai kyau a gaba.
Wani saurayi dan Najeriya mai dauke da shafin Twitter @sarnchos a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, ya bayyana yadda wani bahaushe mai kirki ya kasance mai aminci ga danginsa kusan shekaru 30.
KU KARANTA KUMA: Hotunan gida mai ɗaki daya da ake bayar da shi haya kan N16m a Abuja ya jawo cece kuce
A cikin wallafar farko da ya yi a cikin 2019, ya rubutu yadda mutumin da ya haura shekaru 90 a lokacin yake ta kula da dukiyar mahaifinsa tun bayan rasuwar mahaifin nasa a 1992.
@sarnchos ya bayyana cewa tsawon wadannan shekarun, bai taba karbar wani albashi ba amma ya ciyar da kansa daga abubuwan da ya shuka a filin.
Mutumin wanda abin nasa ya burge shi ya ce bai san ta yaya zai saka wa mutumin mai amana ba.
KU KARANTA KUMA: Burina shine in auri mata 20 - Mutumin da ya auri mata 12 ya haifar da cece-kuce a sabon bidiyo
A shekarar 2021, dan ya nakalto wadancan sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a shekarar 2019 sannan ya ce tsohon zai koma mahaifarsa a jihar Kano.
Baba, kamar yadda ake kiran sa, ya fadawa @sarnchos cewa aikin sa ya kare tunda ya kammala kyakkyawan aiki na kare filin.
Kalli wallafarsa a kasa:
Legit.ng ta tattaro wasu martani a kasa:
@LocaleMann ya ba da shawara:
"Don Allah, yi ƙoƙari ka tura wani ko aƙalla, ɗaya daga cikin yaransa makaranta, a matsayin abin tunawa ga Baba."
@okbabalola ya ce:
"Dan Allah ka mayar da shi gida a jirgin sama- shin yana da lafiyar yin tafiya a mota? Ina ganin zai fi kyau ka mayar da shi gida a jirgin sama."
@kolawoleakinset ya ce:
"Na samu nishadi ta hanyar karanta wannan. Irin wannan kauna da kulawa, ba kasafai suke faruwa ba, har mutum ya ji dadi a cikin zuciyarsa, idan ka gan shi. Da fatan Allah ya saka masa da koshin lafiya, farin ciki, ci gaba da wadatar zuciya da jin dadi, har zuwa sauran rayuwarsa. Mun gode da ka nuna godiya kaima."
@yumlat ya ce:
"Na kusan yin kuka da karanta wannan, hakan ya taba zuciyana, ina matukar girmama biyayya kuma ina matukar girmama mutane masu biyayya, Allah na tare da baba koyaushe. Sai wata rana ita ce kalma mafi wuya."
A wani labarin, mai alfarma Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar III da Ooni na kasar Ife, Oba Adeyeye sun yi kira ga gwamnati ta sake dabara wajen yakar matsalar rashin tsaro.
Da suke magana jiya, manyan sarakunan sun bayyana cewa ba zai yiwu gwamnatin tarayya ta cigaba da amfani da dabara daya, ta na tunanin ta ga sauyi ba.
Jaridar The Nation ta ce Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a rage surutu, a dage da aiki.
Asali: Legit.ng