Yan sanda sun kama barawon da ke shiga gidaje yana sata a zuwan fatalwa

Yan sanda sun kama barawon da ke shiga gidaje yana sata a zuwan fatalwa

- Wani barawo ya shiga hannun ‘yan sanda a Zimbabwe bayan ya yi sata a wasu gidaje ta hanyar sanya wani kaya mai ban tsoro

- Wani shafin Facebook ne ya bayyana hakan inda ya wallafa hotunan wanda ake zargin a dandalin sada zumuntan

- Masu amfani da shafukan sada zumunta sun kasa daina dariya bayan hotunan wanda ake zargin sun yadu a yanar gizo

'Yan sanda a Zimbabwe sun cafke wani barawo bayan ya badda kama a zuwan fatalwa don yin sata a gidajen mutane.

A cewar wani shafin Facebook, General Chiwenga Wisdom, saurayin ya kan kutsa kai cikin gidajen mutane cikin dare sannan ya tsoratar da mazauna gidan wadanda ke cin na kare bayan sun ganshi.

Daga nan sai ya ci gaba da kwashe kayayyaki masu amfani bayan ya yi nasarar tsoratar da wadanda abin ya shafa.

KU KARANTA KUMA: Hotunan sabuwar budurwar Femi Fani-Kayode ya bayyana bayan ya rabu da matarsa ta 4

Yan sanda sun kama barawon da ke shiga gidaje yana sata a zuwa fatalwa
Yan sanda sun kama barawon da ke shiga gidaje yana sata a zuwa fatalwa Hoto: General Chiwenga Wisdom
Asali: Facebook

Shafin ya rubuta:

"An kama barawo a Gutu ya kasance yana kutsawa cikin gidaje cikin dare yana nuna kamar shi fatalwa ne kuma idan masu zama a gidajen suka gudu sai ya yi sata."

KU KARANTA KUMA: Magidanci ya gwangwaje matarsa da motoci 2 da yawon jirgin sama ranar zagayowar haihuwarta

Yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta sun kasa gaskata idanunsu kuma sun mamaye sashen sharhi na rubutun da tunaninsu.

Jay J. Mwenesani ya ce:

"Abin baƙin ciki! Samfurin ƙasar da ta gaza - ya kamata ya kasance a makaranta ko kuma ya sami hanyar samun kuɗi don tafiyar da rayuwarsa. Baƙin cikin da ke a idanunsa - mai yiwuwa yana jin yunwa."

Admire Machingura ya yi sharhi:

"Na zargi zanu pf. Ya kama ace ya zama lauya ko likita amma an sace makomarsa."

Onalenna Dolph Sibanda ta ce:

"Gaskiya mutum ya cancanci lambar yabo na zinare."

A wani labarin, rundunar yan sanda ta kori yan bindiga yayin da suka kai hari ƙauyen Dangeza, ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da kakakin rundunar jihar, SP Gambo Isa, ya fitar a jihar Katsina, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Yace: "Ranar Laraba da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, DPO na Batsari ya jagoranci tawagar jami'an yan sanda zuwa ƙauyen Dangeza, suka fatattaki wasu yan bindiga da suka yi ƙoƙarin kai hari ga mazauna garin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel