Hotunan sabuwar budurwar Femi Fani-Kayode ya bayyana bayan ya rabu da matarsa ta 4

Hotunan sabuwar budurwar Femi Fani-Kayode ya bayyana bayan ya rabu da matarsa ta 4

- Da alama tsohon ministan sufurin jirgin sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode, ya sake fadawa kogin soyayya

- A cewar rahotanni, wata tsohuwar sarauniyar kyau, Miss Ezenwa Chika Nerita ita ce budurwar dan siyasar yanzu

- An hango sabuwar budurwar FFK a bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yan ukun dan siyasar wanda ya haifa tare da matarsa ​​ta hudu, Precious Chikwendu

- Wannan na zuwa yan watanni bayan FFK da Precious sun tabbatar da cewa alakar su ba ta gyaruwa

Ga dukkan alamu, dan siyasar Najeriya, Femi Fani-Kayode, ya sake baiwa soyayya wata dama kuma bai bata lokaci ba wajen nuna sabuwar masoyiyar tasa.

A cewar rahotanni daga LIB, tsohon ministan sufurin jirgin saman ya nuna sha'awar Sarauniyar kyau ta 2019/2020, Miss Ezenwa Chika Nerita.

KU KARANTA KUMA: Hotunan gida mai ɗaki daya da ake bayar da shi haya kan N16m a Abuja ya jawo cece kuce

Hotunan sabuwar budurwar Femi Fani-Kayode ya bayyana bayan ya rabu da matarsa ta 4
Hotunan sabuwar budurwar Femi Fani-Kayode ya bayyana bayan ya rabu da matarsa ta 4 Hoto: @lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

An tattaro cewa Nerita ta hallara kuma ta zage a yayin bikin zagayowar ranar haihuwar ‘yan ukun dan siyasar wanda ya haifa tare da tsohuwar matar sa, Precious Chikwendu.

Duba hotunan sabuwar budurwar FFK a kasa:

A kwanakin baya ne FFK ya raba hanya da mahaifiyar 'ya'yansa maza hudu, Aiden, Ragnar, Liam da Aragorn, duk da cewa ita ce matarsa ​​ta huɗu.

KU KARANTA KUMA: Riƙon alƙawari: Tsawon shekaru 30 Bahaushe na kula da dukiyar Bayarabe, ya damƙata ga magada

Rabuwar su ta kasance tare da zarge-zarge a kafofin watsa labarai.

Karanta tsokaci daga masu amfani da intanet game da sabuwar budurwar FFK a ƙasa:

Likee_mercy:

"Wannan ta sake tura kai bayan ta ga babbar sandar da ya yi amfani da ita wajen zane matan da suka gabata Allah ya kyauta."

Edem_rose:

"Lol..wannan matan basu taba koyan darasi .. Duk da haka Allah ya bata sa’a."

Patrashakes90:

"Wadannan 'yan matan basa koyan abu."

Strut_those_heels:

"Har yanzu hoton dangi tare da tsohuwar matar da yara yana rataye a bango lol."

Emesianna:

"Dama kada na ji pim daga gareta game da cin zarafi da sauransu."

A wani labarin, wani magidanci ya bayyana cewa babban burinsa shine ya kara auren wasu matan duk da cewa tuni yana da 12.

Mutumin da ba a san kowanene ba, wanda ke alfahari da auren mata fiye da daya, a cikin wani bidiyo da @kingtundeednut ya wallafa a shafin Instagram, ya ce ya fara ne da mata daya amma ya yi la’akari da auren mata fiye da daya bayan ya samu wadatar dukiya.

Uwargidarsa da suka zauna tare tsawon shekaru 16 ta bayyana shi a matsayin mutum mai nuna kauna da kulawa. Ta ce ta yi mamaki ranar da ya sanar da ita shawarar da ya yanke na kawo wata matar amma ta yarda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel