Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara

Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara

- Jami'an hadin guiwa da suka hada da 'yan sanda tare da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara

- Sun gaggauta bayyana bayan kiran da suka samu na cewa 'yan bindiga na kai hari Hayin Daudu dake Gusau

- Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar yace sun yi musayar wuta inda suka kashe 10 sannan wasu suka tsere da raunika

Jami'an 'yan sanda da kungiyar 'yan sa kai dake Hayin Daudu a garin Gusau na jihar Zamfara sun halaka 'yan bindiga 10 a ranar Litinin.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya sanar da cewa 'yan sanda da 'yan sa kai sun gaggauta zuwa inda aka kira su sakamakon harin da 'yan bindigan ke kaiwa Hayin Daudu, Premium Times ta ruwaito.

"'Yan sandan da aka tura yankin Mada, sun hadu da wata kungiyar sa kai wurin karfe 11 na dare inda suka yi gaggawar zuwa Kauyen Hayin Daudu sakamakon kiran gaggawa da suka samu.

KU KARANTA: Shugaba Kim Jong-un ya haramta saka ɗamammun wanduna da askin banza a kasarsa

Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara
Nasara daga Allah: 'Yan sanda da 'yan sa kai sun sheke 'yan bindiga 10 a Zamfara. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

"'Yan bindigan na dauke da miyagun makamai amma an yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron. A sakamakon haka aka halaka 'yan bindiga 10 yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika," kakakin ya kara da cewa.

Yace 'yan sanda sun tsananta sintiri domin kare rayuka da kadarorin yankunan da ake kai hare-hare kuma za a cigaba da matsantawa 'yan bindigan da duk wasu masu laifi a jihar.

KU KARANTA: Buhari ya dage taron majalisar zartarwa, yana makokin Attahiru da sauran jami'an soji

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'Yan sanda na kira ga jama'a da su basu hadin kai domin kawo karshen wannan matsalar ta ta'addanci.

"Komai ya koma daidai a yankin da lamarin ya shafa kuma jami'an tsaro na cigaba da tsananta sintiri domin gujewa aukuwar wani harin a yankunan," takardar tace.

“Kwamishinan 'yan sandan jihar ya jinjinawa kokarin 'yan sa kan da sauran masu taimakawa wurin yaki da ta'addanci kuma ya bukacesu da su cigaba da aikinsu," Shehu yace.

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Jigawa sun cafke wasu mutum biyar da ake zargi da kaiwa Malam yakubu Ibrahim hari, shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Dutse.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Usman Gomna, ya tabbatar da kamen ga manema labarai a garin Dutse a ranar Laraba, The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan 'yan sandan yayi bayanin cewa wadanda ake zargin sun kutsa sakateriyar jam'iyyar dake karamar hukumar yayin wani taro da aka yi a ranar Litinin inda suka saka karfin tuwo suka dauka shugaban jam'iyyar zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel