Matasa sun kone mahaukaciya bayan kama ta da suka yi da makamai a Legas

Matasa sun kone mahaukaciya bayan kama ta da suka yi da makamai a Legas

- Matasa a yankin Abule Ado dake jihar Legas sun bankawa mahaukaciya wuta bayan kamata da jaririyar sata tare da AK 47 uku

- Sai dai 'yan sandan jihar Legas sun tabbatar da cewa kisan kai matasan suka yi domin basu ga AK 47 din da jaririyar ba

- Kamar yadda aka tabbatar, mahaukaciyar ta kwashe shekaru a yankin kuma tana kwana kasan gada ne

Fusatattun jama'a sun bankawa wata mahaukaciya wuta a yankin Abule Ado dake jihar Legas a ranar Litinin, 'yan sanda suka tabbatar.

Matar da aka kone an kama ta da jaririyar sata da kuma bindiga kirar AK 47 guda uku kafin a kasheta, Premium Times ta ruwaito.

Amma 'yan sanda sun kwatanta lamarin da kisan kai tare da daukan hukunci a hannu domin ba a samu jaririyar ko makaman daga mahaukaciyar ba.

Muyiwa Adejobi, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Legas a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, yace sun fara bincike a kan lamarin da zummar cafke wadanda ake zargi da kisan kan, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo: Fadar Shugaban Kasa ta Magantu

Matasa sun kone mahaukaciya bayan kama ta da suka yi da makamai a Legas
Matasa sun kone mahaukaciya bayan kama ta da suka yi da makamai a Legas. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Soja da ya rasu a hatsarin jirgin sama ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da littatafai

"Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta fara bincike kan kisa tare da kone wata mahaukaciya da aka kama da jaririyar sata da kuma bindigogi kirar AK 47 uku a Abule Ado, karkashin gada ta yankin Festac dake jihar Legas a ranar Litinin a ranar 24 ga watan Mayun 2021.

"Dogaro da binciken farko, an gano cewa mahaukaciyar na zama a yankin na tsawon shekaru kuma wasu bata gari a yankin ne suka banka mata wuta bayan kamata da jaririya tare da AK 47 uku.

"Rundunar na sanar da cewa matar da aka kona ya bayyana cewa bata tare da jaririya kuma babu AK 47 a hannunta. 'Yan sanda zasu cigaba da bincike kuma za a gano wadanda suka yi kisan kan," 'yan sandan suka ce.

A wani labari na daban, Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bada umarnin dage taron majalisar zartarwa da ake yi a ranar Laraban kowanne mako.

Ya kara da mayar da taron majalisar 'yan sanda da za a yi a wannan Alhamis mai zuwa har zuwa ranar Alhamis ta makon gaba.

Kamar yadda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya sanar, wannan dagewan an yi ta ne domin karrama tsohon shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami'ai goma da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin sama da suka yi a ranar Juma'a a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel