Rikicin shugabanci: ISWAP sun kama kwamandojin Shekau, sun gana da wadanda suka yi mabaya'a

Rikicin shugabanci: ISWAP sun kama kwamandojin Shekau, sun gana da wadanda suka yi mabaya'a

- 'Yan ta'addan ISWAP na cigaba da kamawa tare da kashe mayakan Boko Haram na bangaren Shekau a Sambisa

- A halin yanzu, manyan kwamandojin Shekau da suka mika wuya suna ganawa da shugabannin ISWAP

- Kamar yadda aka gano, ISWAP ta sha alwashin kawar da dukkan mabiya Abubakar Shekau matukar basu yi mubaya'a ba

Mayakan ISWAP sun cigaba da tsanantawa bangaren Boko Haram na Abubakar Shekau, suna ta kashe-kashe tare da kama wasu daga cikin kwamandojin bangaren, majiyoyi da suka san abinda ke faruwa cikin 'yan ta'addan suka tabbatar.

Sun kara da kama manyan kwamandojin Shekau kamar su Mustapha Krimima Jaysh, Ba'akaka, Malkin Tijjani, Hirasama da Mallam Ballu wadanda suka ki mika wuya kuma suka yi yunkurin tserewa, Vanguard ta ruwaito.

Majiyar tace an kama da yawan 'yan ta'addan dake kan motocin yaki wadanda aka gani a Marte, gabas da Tumour, Tumbumma da Tumbuktu duk a Sambisa bayan musayar ruwan wuta da aka yi tsakanin ISWAP da Boko Haram na bangaren Shekau a Garin Malam.

KU KARANTA: Soja da ya rasu a hatsarin jirgin sama ya shirya rabawa marayu kayan makaranta da littatafai

Rikicin shugabanci: ISWAP sun sake kwamandojin Shekau, sun gana da wadanda suka yi mabaya'a
Rikicin shugabanci: ISWAP sun sake kwamandojin Shekau, sun gana da wadanda suka yi mabaya'a. Hoto daga @HumAngle
Asali: UGC

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ana cigaba da jerin taruka a sansanin Sabeel Huda dake tsakiyar dajin Sambisa tsakanin kwamandojin ISWAP da wasu jiga-jigan Boko Haram da suka mika wuya.

An tattaro cewa kwamitin ladabtawa na Albarnawy ne zai sanar da makomar kwamandoji da mayakan Boko Haram da suka cafke, inda yake samun shugabancin Muhammad Malumma, babban alkalin ISWAP.

Shugabannin ISWAP sun sha alwashin karar da dukkan mayakan Shekau matukar basu yi mubaya'a ba.

Wasu bayanan sirri wadanda aka samu daga waya tsakanin shugabannin ISWAP biyu ya bayyana cewa akwai kwamiti wanda ke samun shugabancin Abu-Mosad Albarnawy, wanda shugaban ISIS ya nada domin rushe dukkan shugabanci da shugabanni da Shekau din Boko Haram ya nada.

An kara da gano cewa wani Walin ISWAP, Muhammad Dawud, wanda aka fi sani da Abu Hafsat tare da wasu hafsoshin yakinsu da kwamandoji daga yankin tafkin Chadi, Timbuktu da Marte ne ke shirya komai na yakin.

KU KARANTA: Shugaba Kim Jong-un ya haramta saka ɗamammun wanduna da askin banza a kasarsa

A wani labari na daban, Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bada umarnin dage taron majalisar zartarwa da ake yi a ranar Laraban kowanne mako.

Ya kara da mayar da taron majalisar 'yan sanda da za a yi a wannan Alhamis mai zuwa har zuwa ranar Alhamis ta makon gaba.

Kamar yadda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya sanar, wannan dagewan an yi ta ne domin karrama tsohon shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami'ai goma da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin sama da suka yi a ranar Juma'a a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel