Masarautar Katsina ta nada Jastis Adamu Bello a matsayin sabon Hakimin Kankara

Masarautar Katsina ta nada Jastis Adamu Bello a matsayin sabon Hakimin Kankara

- Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman Mai Shari'a Adamu Bello mai -ritaya a matsayin sabon hakimin Kankara

- Hakan ya biyo bayan samun amincewar da Gwamnatin Jihar Katsina a cikin wata wasika zuwa ga masarautar

- Nadin nasa na zuwa ne bayan tube rawanin tsohon Hakimi, Alhaji Yusuf Lawal, bisa zargin alaka da 'yan fashi

Biyo bayan sallamar tsohon Hakimin garin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, bisa zargin yana da alaka da 'yan fashi, majalisar masarautar Katsina ta amince da nadin Mai Shari'a Adamu Bello mai ritaya a matsayin sabon hakimin.

A wata wasikar nadin dauke da sa hannun mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, nadin ya biyo bayan amincewar da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi ne kamar yadda yake kunshe a cikin wata wasika da aka aika wa masarautar mai dauke da lamba S / SGKT / 77 / S.2 / VOL.II / 207 a ranar 24 ga Mayu 2021, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Burina shine in auri mata 20 - Mutumin da ya auri mata 12 ya haifar da cece-kuce a sabon bidiyo

Masarautar Katsina ta nada Jastis Adamu Bello a matsayin sabon Hakimin Kankara
Masarautar Katsina ta nada Jastis Adamu Bello a matsayin sabon Hakimin Kankara Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ku tuna cewa masarautar ta sanar da korar Sarkin Pauwan Katsina, Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal kan zargin alaka da yan fashi.

Sakataren Majalisar Masarautar, Sarkin Yakin Katsina, Alhaji Bello Mamman-Ifo, ya fadawa manema labarai cewa an samu basaraken da laifin duk tuhumar da ake masa, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kakakin masarautar, Sarkin Labarai, Alhaji Ibrahim Bindawa, ya kuma tabbatar da cewa Sarkin na Katsina ya ba da umarnin sallamar hakimin bayan ya karbi rahoton kwamiti.

A baya Legit.ng ta kawo cewa majalisar sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ta tumɓuke rawanin hakimin ƙanƙara biyo bayan gano cewa yana da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa yan bindiga.

Katsina Daily post ta wallafa a shafinta na facebook cewa masarautar ta gano sarkin Pauwan Katsina kuma hakimin ƙanƙara, Alhaji Yusuf Lawal yana taimaka wa wasu yan bindiga wajen gudanar da ayyukan ta'addacin su.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-duminsa: Tsohon dan takarar Shugaban kasa ya sauya sheka zuwa PDP gabannin 2023

Bisa wannan dalilin ne majalisar sarki ta tsige shi daga muƙaminsa na Sarkin Pauwa hakimin kankara kwata-kwata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel