Da dumi-duminsa: Tsohon dan takarar Shugaban kasa ya sauya sheka zuwa PDP gabannin 2023
- Jam’iyyar PDP ta kara samun karfi yayin da tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas, Donald Duke, ya shiga jam’iyyar
- An tabbatar da dawowar Duke zuwa PDP a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, yan kwanaki bayan ana ta rade-radi
- Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamna Ayade ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC
Donald Duke, tsohon gwamnan jihar Kuros Riba ya koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), jaridar The Punch ta ruwaito.
Jaridar ta ruwaito cewa shugaban kwamitin riko na PDP a jihar ta kudu maso kudu, Effiok Cobham, ya bayyana hakan a ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, a wani taron manema labarai a Calabar.
KU KARANTA KUMA: Ku yi ku gama: Sabon tsarin APC ba zai hana Tinubu zama shugaban ƙasa a 2023 ba, cewar wani jigo
Lokacin da aka tambaye shi don tabbatar da jita-jitar cewa tsohon gwamnan ya koma jam'iyyar, sai ya ce:
"Ee, ya yi rajista."
Legit.ng ta lura cewa Duke ya kasance a cikin PDP har zuwa 2008 lokacin da ya fice zuwa Social Democratic Party (SDP) inda ya fito a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2019.
Ya yi gwamna sau biyu na Kuros Riba tsakanin 1999 da 2007.
KU KARANTA KUMA: Ban Ji Dadi Ba: Shugaba Buhari Ya Shiga Jimamin Kifewar Jirgin Ruwa a Kebbi
Jaridar The Cable ta kuma ruwaito cewa Donald Duke, ya ce ya koma jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar 2020.
Ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda “lema tana yagewa”.
A wata sanarwa a ranar Laraba, Duke ya ce Ben Ayade, gwamnan jihar, shine ya bukace shi da ya koma PDP, ya kara da cewa abin takaici ne gwamnan ya fice daga jam'iyyar.
A halin yanzu, sabon ci gaban ya biyo bayan sauya sheka da Gwamna Ben Ayade yayi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress.
A gefe guda, mun ji cewa Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ya bayyana sauya shekar gwamnan Kross Riba, Ben Ayade, zuwa jam'iyar All Progressives Congress (APC) ya girgizasu kuma yayi matukar basu kunya.
Gwamna Ishaku ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban ma'aikatar Aso Rock, Farfesa Ibrahim Gambari ranar Juma'a, rahoton DT.
Ishaku yace: "Ba san abinda yake tunani ba, saboda mun yi matukar girgiza da fitarsa daga jam'iyyarmu zuwa APC, saboda dukkanmu na ganin PDP matsayin mafita daga APC."
Asali: Legit.ng