Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa

Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa

- Jami'an hukumar yan sanda sun yi ram da wani jami'in soji da ake zarginsa da kashe ɗan kasuwa a ƙaramar hukumar Ikot Abasi

- Mai motar da aka kashe ya ɗauki sojan ne domin ya rage masa hanya ba tare da sanin kashe shi zai yi ba

- Yan sanda sun bibiyi inda motar take sannan suka je suka kamo jami'in sojin tare da ƙwato motar mamacin

Rundunar yan sanda ta damƙe wani jami'in sojin Najeriya da take zargin yana da hannu a kisan wani shahararren ɗan kasuwa a ƙaramar hukumar Ikot Abasi jihar Akwa Ibom.

KARANTA ANAN: Bayan Mutuwar COAS Attahiru, FG Ta Bayyana Ranar da Wasu Sabbin Jirgaen Yaƙi Zasu Iso Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa jami'in ya kashe shi sannan ya jefad da shi a gefen titi bayan mutumin ya ɗauke shi a motarsa ranar Lahadi.

Wata majiya mai ƙarfi a ƙaramar hukumar Ikot Basi ta faɗawa wakilin Punch cewa an bibiyi inda jami'in sojin yake kuma an kama shi, da motar mamacin, sannan an samu bindiga a tare da shi.

Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa
Rundunar Yan Sanda Ta Yi Ram da Jami’in Soji Kan Kashe Wani Hamshaƙin Ɗan Kasuwa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Majiyar tace: "Lamarin ya faru ranar Lahadi, wani direban mota ya taimaka ya ɗauki jami'in soja ba tare da sanin cewa kashe shi zai yi ba. Sai da suka je wani wuri sojan ya kashe shi kuma ya jefar da gawarshi a gefen titi."

"Jami'an yan sanda sun gano inda gawar take, sannan suka kai ta ɗakin ajiye gawarwaki, wannan duk ya faru ne ranar Lahadi."

KARANTA ANAN: Taɓarɓarewar Tsaro: CUPP Ta Buƙaci Shugaba Buhari Yayi Murabus

"A ranar Litinin, yan uwan wanda aka kashe suka kai ƙara ofishin yan sanda na Ikot Abasi, kuma aka yi sa'a motar mamacin tana da na'urar dake nuna zirga-zirgar ta, yan sanda suka bibiyi inda take kuma suka gano ta a ƙaramar hukumar Ukanafun."

"Jami'an yan sandan suka dira wurin suka mamaye shi, suka yi ram da jami'in sojin, suka ƙwato motar da kuma bindiga ƙirar AK-47." Inji majiyar.

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda ta jihar Akwa Ibom, Odiko Macdon, yace lamarin yana ƙarƙarshin bincike.

A wani labarin kuma Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya bayyana cewa sai an magance talauci a Najeriya sannan za'a samu tsaro.

Sanatan yace rashin adalci da Talauci sune suka haifar da duk wannan ƙalubalen tsaron da ƙasar take fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel