'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10, Sun Wasu Sace Da Dama a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10, Sun Wasu Sace Da Dama a Zamfara

- Ƴan bindiga sun afka wasu ƙauyuka a jihar Zamfara sun kashe mutum 10 sun sace wasu kayayyaki

- Ƴan sanda tare da ƴan-sakai na wasu ƙauyukan sun yi haɗin gwiwa sun fafata da su sun kashe 10

- Sai dai kakakin ƴan sandan jihar Zamfara ya ce ƴan sanda da ƴan sa-kai sunyi musayar wuta da su sun kashe 10

Ƴan bindiga sun kashe mutane 10 sun kuma sace wasu da dama a ƙauyuka biyar da ke ƙaramar hukumar Bungudu na jihar Zamfara, The Punch ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Musa Sani, ya ce ƴan bindigan da suka zo a kan babura sun shiga ƙauyukan Dandamji, Gidan Runji, Doka, Yanmadanga da Yarkatsina a yammacin ranar Litinin.

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10, Sun Wasu Sace Da Dama a Zamfara
'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10, Sun Wasu Sace Da Dama a Zamfara. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan Sanda Sun Kama Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin 'Brekete Family'

Sani ya ce yan bindigan sun kuma sace dabbobi masu ɗimbin yawa.

Ya ce ƴan bindigan sun shafe lokaci mai tsawo suna cin karen su babu babbaka saboda rashin jami'an tsaro.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara, CP Mohammed Shehu, ya tabbatar da kashe mutum 10, ya ƙara da cewa an kuma kashe ƴan bindiga 10 a harin.

Ya ce, "misalin ƙarfe 11 na daren ranar Litinin, yan sandan da ke Mada tare da ƴan sa-kai na ƙauyen Hayin Daudu da kewaye a yankin Mada a ƙaramar hukumar Gusau, sun amsa kiran neman ɗauki daga ƙauyen sakamakon ƴan bindiga da dama da suka shiga garin da nufin kaiwa mutanen ƙauyen hari.

"Ƴan bindigan na ɗauke da muggan makamai kuma sunyi musayar wuta da ƴan sanda/ƴan sa-kai, ƴan bindiga 10 sun mutu yayin da saura suka tsere da raunin bindiga.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban Matasa na APC a Kofar Gidanta

"Tuni dai komai ya koma yadda ya ke a garin yayin da ƴan sanda ke sintiri domin kare afkuwar wani harin.

"Kwamishinan ƴan sanda ya yaba da ƙoƙarin ƴan sa-kai da wasu wadanda ke taimakawa wurin yaƙi da laifuka yana mai kira su cigaba da hakan".

A wani labarin rahoton daban, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya zargi tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu da zaman ɗan leƙen asiri da matsala ga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da ya ke magana a gidan gwamnati a Port Harcourt a ranar Litinin, Wike ya ce Aliyu mutum ne da ya daɗe yana yaudarar jam'iyyarsu ta PDP ya kuma yi mata zagon ƙasa an 2015, The Nation ta ruwaito. Wike Ya Ce Aliyu 'Ɗan Leƙen Asiri' Ne Kuma Alaƙaƙai Ne Ga PDP.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan wata hira da aka yi da Aliyu a jaridun ƙasa idan ya zargi Wike da ƙoƙarin mayar da kansa uban jam'iyya kuma kai mulkin kama karya a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel