Jami'an Tsaro Sun Cafke Yan Bindiga 37 Dake Shirin Kai Hari INEC da Ofshin Yan Sanda
- Sabbin jami'an tsaron yankin kudu maso gabas, Ebubeagu, sun cafke mutum 37 da zargin suna shirin kai hari ga jami'an tsaro
- Kwamishinan tsaron jihar Ebonyi, Stanley Okoro-Emegha, shine ya bayyana haka Ranar Litinin a Abakalike
- Kwamishinan yace sun miƙa wa rundunar yan sanda mutanen da aka kama domin gudanar da bincike
Jami'in gwamnatin jihar Ebonyi ya bayyana cewa sabbin jami'an tsaron yankin kudu-gabas 'Ebubeagu' sun cafke mutum 37 da ake zargi suna shirin kai hari ofishin yan sanda da INEC a jihar.
KARANTA ANAN: Tankar Man Fetur Ta Fashe a Jihar Lagos, Mutane da Dama Sun Sha da Ƙyar
Kwamishinan tsaro, Stanley Okoro-Emegha, shine ya bayyana wa manema labarai haka a Abakalike ranar Litinin, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
Yace an kama waɗanda ake zargin ne a garin Agubia, ƙaramar hukumar Ikwa ranar Lahadi.
Rahoton thisday live ya nuna cewa an kama waɗan da ake zargin ne bayan samun wasu bayanan sirri cewa mutanen na shirye-shiryen kai hari ofishin INEC da caji ofis na ƙaramar hukumar Ikwa.
Kwamishinan yace: "A wani aiki da jami'an tsaron Ebubeagu suka fita da tsakar daren Lahadi, sun sami nasarar damke wasu bara gurbi 37 a Agubia dake ƙaramar hukumar Ikwa."
"Sun sami nasarar ne da haɗin guiwar shugaban ƙaramar hukumar Ikwa, Steve Orogwu, da kuma jami'an tsaron dake ofishin hukumar yanda na Ikwa."
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari: Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli
Ya ƙara da cewa waɗan da aka kama ɗin yan asalin jihar ne da wasu da suka fito daga sassa daban-daban na yankin kudu maso gabas.
Yace: "Wasu daga cikin mutanen ba yan jihar Ebonyi bane, amma mun miƙa su ga hukumar yan sanda domin gudanar da bincike"
"Daga cikin abubuwan da aka ƙwato a hannun su akwai taswirar yankin da suke shirin kai hari, wanda ya haɗa da ofishin yan sanda da wasu ofisoshin hukumar zaɓe INEC."
A wani labarin kuma Sarki Salman Ya Kira Shugaba Buhari Ta Wayar Salula, Ya Masa Ta'aziyyar Mutuwar Janar Attahiru
Sarki Salman na ƙasar Saudiya yayi wa shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ta'aziyyar mutuwar shugaban sojin ƙasa, Janar Attahiru, ta wayar salula.
Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sada zumunta.
Asali: Legit.ng