Kada a Soke NYSC, a Horar da Matasa Kamar Sojoji Su Tunkari Matsalar Rashin Tsaro

Kada a Soke NYSC, a Horar da Matasa Kamar Sojoji Su Tunkari Matsalar Rashin Tsaro

- Shehu Sani ya yi tsokaci kan yunkurin majalisar wakilai na soke yin bautar kasa a Najeriya

- Shehu Sani ya ce, kamata ya yi a horar da matasa su tunkari lamarin rashin tsaron da ake fama

- Matsalar tsaro na ci gaba da ta'azzara a Najeriya, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dama

Shehu Sani, ya yi sharhi kan kudurin majalisar wakilai na dakatar da yi wa kasa hidima a karkashin shirin NYSC da aka saba a Najeriya.

Rahoto ya bayyana cewa, majalisar wakilai ta yi zama na biyu kan yunkurin soke shirin bautar kasa a Najeriya kwata-kwata.

Shehu Sani, wanda yake tsohon sanata mai wakilatar Kaduna ta tsakiya, ya bayyana haka a daren Litinin 24 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Minista a Zamanin Sardauna, Danburam-Jada, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kada a Soke NYSC, a Horar da Matasa Kamar Sojoji Su Tunkari Matsalar Rashin Tsaro
Kada a Soke NYSC, a Horar da Matasa Kamar Sojoji Su Tunkari Matsalar Rashin Tsaro Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Tuwita, ya ce sam ba daidai bane soke bautan kasa a Najeriya ba, sai dai ma a gyara shirin, duba da wasu abubuwa da ya bayyana.

Ya dage cewa, wasu matasan Najeriya basu taba barin garuruwansu zuwa wasu wurarensu ba ko jami'o'insu. Wannan yasa ya kamata a fadada ayyukan bautan kasa saboda ba matasa damar sanin zamantakewa a wasu yankuna.

A cewarsa: "Bai kamata a soke NYSC ba. Ana bukatarsa yanzu fiye da kowane lokaci. Yawancin 'yan Najeriya ba su taba sanin ko'ina ba face garin su da garin Jami'a in ba dalilin NYSC ba. Yakamata a fadada aikin don baiwa cikakken horon soja a cikin halin rashin tsaro."

Rashin tsaro a Najeriya na kara tabarbarewa, lamarin da ya jawo mace-macen al'ummomi da dama, musamman yankin arewacin Najeriya.

KU KARANTA: An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa

A wani labarin, Majalisar Wakilai na duba yiwuwar dakatar da shirin bautar Kasa na NYSC, jaridar Punch ta ruwaito.

Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya na Canji shekarar 2020, wanda ke neman soke dokar NYSC, an gabatar da shi a karatu na biyu.

Wanda ya dauki nauyin yunkurin, Mista Awaji-Inombek Abiante, a cikin bayanin shawarar, ya zayyana dalilai daban-daban da za su sa a soke NYSC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel