Dole mulki ya bar Yankin Arewa bayan wa’adin Buhari – Jigon APC ya na goyon ‘Yan Kudu

Dole mulki ya bar Yankin Arewa bayan wa’adin Buhari – Jigon APC ya na goyon ‘Yan Kudu

- A 2023, Mohammed Bello Mustapha ya na ganin ‘Yan Kudu suka dace da mulki

- Mohammed Mustapha ya ce wannan ita ce tsarin da aka taho a kai tun 2013/2014

- Babban jigon na jam’iyyar APC ya ce yin hakan ne zai tabbatar da zaman lafiya

A ranar Litinin, daya daga cikin ‘yan takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Mohammed Bello Mustapha, ya tabo maganar 2023.

Jaridar The Nation ta ce Mohammed Bello Mustapha ya yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki ta goyi bayan shugabancin kasar nan ya koma kudu.

Tsohon ‘dan takarar gwamnan na jihar Taraba a karkashin jam’iyyar CPC a 2011 ya ce wadanda suka kafa APC sun zauna sun yi wannan alkawari.

Kara karanta wannan

2023: Babban Jigon PDP Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi, Ya Koma Jam’iyyar LP

KU KARANTA: Mataimakin Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Esu, ya shiga APC

Barista Mohammed Mustapha ya na da ra’ayin cewa lokaci ya yi ‘dan kudu ya zama shugaban kasa tun da Muhammadu Buhari ya yi wa’adi biyu.

Da yake magana da ‘yan jarida a Legas, ‘dan takarar kujerar shugaban jam’yyar ya ce adalci da son gaskiya shi ne a ba mutanen kudu shugabanci a APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce: “An samu fahimta wanda dukkanmu mun san da zaman lokacin da aka kafa jam’iyyarmu a 2013/2014 cewa za a rika zagayawa da mulki.”

“Idan na ce mulki, ina nufin shugabancin kasa da jagorancin jam’iyya.” Inji Mohammed Mustapha.

Dole mulki ya bar Yankin Arewa bayan wa’adin Buhari – Jigon APC ya na goyon ‘Yan Kudu
Barr. Muhammad Bello Mustapha Hoto: authenticnewsdaily.wordpress.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Tinubu, shugabannin Yarbawa ba su goyon bayan a kafa kasar Oduduwa

‘Dan siyasar ya nemi a saka wa gudumuwar da manyan jam’iyyar su ka bada wajen kafa APC. Ya ce idan mulki na yawo ne kawai za a samu zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

Daily Trust ta rahoto shi ya na cewa: “Mulkin kasa ya tafi Kudu, shugabancin jam’iyya ya zo Arewa.”

Shugaban matasan kungiyar The Buhari Organisation na farko da aka yi ya kuma yi kira ga manyan jam’iyya su ba matasa dama, a ga gudun ruwansu.

Dazu kun ji cewa maganar da Gwamnan Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, ya yi game da zaben 2023 ta bata ran wasu kusoshin APC a yankin Kudancin Najeriya.

Sanata Bagudu ya fito ya na cewa duk mai sha’awar shugaban kasa zai iya yin takara a 2023, akasin kiran da ake yi na warewa 'Yan siyasar kudu kujerar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel