Kan Bola Tinubu, Gwamnoni da manyan Yarbawa ya hadu, ba su goyon bayan a raba Najeriya

Kan Bola Tinubu, Gwamnoni da manyan Yarbawa ya hadu, ba su goyon bayan a raba Najeriya

- Bola Tinubu da jagororin APC a Kudu maso yamma sun yi taro a Legas

- An kira wannan zama ne domin nuna rashin goyon bayan kiran a barke

- Shugabannin Yarbawa sun yi na’am da hana makiyaya yawo da dabbobi

Yayin da ake kiran a raba Najeriya, ta yadda za a samar da jamhuriyar Oduduwa daga kasar Yarbawa, shugabannin yankin sun yi wani taro.

Jaridar Daily Trust ta ce shugabannin jam’iyyar APC na Kudu maso yamma, sun yi zama a ranar Lahadi, 23 ga watan Mayu, 2021, a garin Legas.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila da sauran shugabannin sun fito sun nuna rashin goyon bayansu game da kiraye-kirayen a raba kasar nan, a cewar BBC.

KU KARANTA: IPOB: 'Yan bindiga sun mamayi Jami’a tsaro, sun kona ofishin INEC

An yi wannan taro na musamman ne a Lagos House, da ke unguwar Marina, a karkashin shugabancin tsohon shugaban APC, Bisi Akande.

Wadanda suka amsa kiran Cif Bisi Akande sun hada da jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da kuma wasu daga cikin gwamnonin APC.

Babajide Sanwo-Olu, Dapo Abiodun da Adegboyega Oyetola duk sun samu halartar zaman. Kayode Fayemi da Rotimi Akeredolu ba su samu zuwa ba.

Sauran wadanda aka gani a taron sun hada da Janar Alani Akinrinade, tsohon gwamna, Aremo Segun Osoba, Otunba Niyi Adebayo da Pius Akinyelure.

KU KARANTA: Osinbajo na nan garau - Fadar Shugaban kasa

Kan Bola Tinubu, Gwamnoni da manyan Yarbawa sun hadu, ba su goyon bayan a raba Najeriya
Bola Tinubu, da sauran manyan Yarbawa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Cif Bisi Akande ya karanto matsayar shugabannin Kudu maso yammacin kasar, inda su kayi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su kawo zaman lafiya.

Ya ce: “Mun fahimci ana fama da matsalar tsaro a kasar nan. Ana fuskantar barazanar ta’addanci da tsageranci a wurare da-dama, wanda hakan yake taba rayuwa da hanyar neman abincin Bayin Allah, mutanen Najeriya masu son zaman lafiya.”

Manyan Yarbawan sun yi tir da yunkurin tada hankali da kiran a bangare, kuma suka nuna goyon-baya a kan matsayar gwamnonin Kudu na hana kiwo.

A baya an ji yadda Ministan shari'a, Abubakar Malamai ya soki matakin haramtawa makiyaya yawo da dabbobi da aka yi a jihohin Kudancin Najeriya.

Kungiyar SLC ta caccaki AGF, Abubakar Malamai SAN, ta ce babu hikima a kamanta yi wa mutane barna a gonakinsu da sana'ar saida karafunan mota.

Asali: Legit.ng

Online view pixel