PDP ta rasa Gwamna, Mataimakin Gwamna da ‘Dan Majalisar Tarayya zuwa APC a cikin kwana 5

PDP ta rasa Gwamna, Mataimakin Gwamna da ‘Dan Majalisar Tarayya zuwa APC a cikin kwana 5

- Mataimakin gwamnan jihar Kuros Riba, Ivara Ejemot Esu, ya bar PDP

- Farfesa Ivara Esu ya sauya-sheka zuwa Jam’iyyar APC cikin makon nan

- Hakan na zuwa ne kusan mako guda bayan Gwamna Ayade ya tafi APC

Mai girma Mataimakin gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ivara Ejemot Esu, ya bada sanarwar cewa ya bar jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Gidan talabijin na AIT ya fitar da rahoto a ranar Litinin, 24 ga watan Mayu, 2021, cewa Farfesa Ivara Ejemot Esu, ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC.

Ivara Ejemot Esu ya tabbatar da cewa ya yi rajista a matsayin cikakken ‘dan jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Gwamna Ben Ayade, ya fita daga PDP, ya koma APC

Mataimakin gwamnan ya dauki wannan mataki ne kwanaki hudu bayan mai gidansa, gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya fice daga jam’iyyar PDP.

Da wannan mataki da Farfesa Ivara Ejemot Esu ya dauka a jiya, ya kawo karshen rade-radin cewa shi da mai gidansa ba su tafiya a kan shafi guda na siyasa.

A wani bidiyo da Channels TV ta wallafa, ta tabbata cewa Ivara Esu yayi ban kwana da jam’iyyar PDP da ta ba su nasarar lashe zabe a 2015 da kuma 2019.

Da yake yin rajista a matsayin ‘dan jam’iyyar APC mai mulki a ofishinsa, Farfesa Ivara Edu ya ce ya na goyon-bayan mai gidansa kan sauya-shekar da ya yi.

PDP ta rasa Gwamna, Mataimakin Gwamna da ‘Dan Majalisar Tarayya zuwa APC a cikin kwana 5
Ivara Ejemot Esu Hoto: Sir Benedict Ayade / Facebook
Asali: Facebook

KU KARANTA: Tsohon Gwamna, Mataimakin Gwamna, Sanata za su kara a Kano a 2023

A cewar Ivara Edu, tun da aka dawo mulkin farar hula a Najeriya shekarar 1999, ba a taba yin lokacin da Kuros Ribas ba ta tare da gwamnatin tarayya ba.

Farfesa Edu yake cewa an san mutanen Kudu maso kudu da zama a jam’iyyar da ke kan mulki.

Da wannan sauyin-sheka, Ivara Edu ya na ganin jihar Kuros Ribas za ta kai ga ci. Watakila hakan ya sa ‘dan majalisa na jihar, Hon. Mike Etaba ya shiga APC.

A shekarar bara, an ji Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade ya amince da nadin mutane 190 a matsayin hadimai masu taimaka masa da masu bada shawara.

Mai girma gwamnan ya bayyana wannan ne ta bakin wani hadiminsa, Christian Ita, ya ce hakan zai sa kowa ya ci ribar gwamnati da romon damukaradiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel