2023: Matsayar Gwamnoni a kan neman kujerar Shugaban kasa ya na shirin hargitsa APC

2023: Matsayar Gwamnoni a kan neman kujerar Shugaban kasa ya na shirin hargitsa APC

- Jawabin da kungiyar gwamnonin APC ta fitar ya raba kan jagororin jam’iyya

- A makon jiya, shugaban PGF, ya ce kofar 2023 a bude ta ke ga kowane bangare

- Wannan magana sam ba tayi wa jiga-jigan APC na Kudancin Najeriya dadi ba

Ana samun baraka a tafiyar APC mai mulki a dalilin budewa kowa kofar takara da gwamnonin jam’iyyar suka yi, Daily Trust ta rahoto wannan dazu.

Jaridar ta bayyana cewa akwai sabani a game da yankin da za a ba kujerar shugaban jam’iyya, da kuma takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A wani jawabi da shugaban kungiyar gwamnonin APC (PGF) , Sanata Senator Atiku Abubakar Bagudu, ya yi, ya ce kowa zai iya neman takara a 2023.

KU KARANTA: Wasu Gwamnonin APC 2 sun kauracewa taron da Bola Tinubu suka kira

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu daga cikin gwamnonin na APC da kusoshin jam’iyya ba su ji dadin kalaman da gwamnan Kebbi ya yi ba.

Rahoton ya ce jawabin shugaban PGF, Atiku Abubakar Bagudu, ya fusata gwamnonin yankin Kudu da suke ganin za su karbi mulkin kasa a 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu kungiyoyi a cikin jam’iyyar APC sun fara shirin yin bore a kan wannan matsaya saboda zargin cewa ana so Arewa ta cigaba da shugabanci.

Wani tsohon ‘dan takarar shugaban kasa kuma jigon APC, Chekwas Okorie, ya ce rigima za ta barke a APC idan ba a kai tikitin takara zuwa Kudu ba.

KU KARANTA: APC ta samu karin Gwamna a Najeriya bayan sauya-shekar Ayade

2023: Matsayar Gwamnoni a kan neman kujerar Shugaban kasa ya na shirin hargista APC
Shugaban PGF, Atiku Bagudu Hoto: @AABagudu
Asali: Twitter

Wannan shi ne ra’ayin Mohammed Bello Mustapha, wanda ya na cikin wadanda su ke neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa a zaben da za ayi.

Jaridar The Nation ta rahoto Otunba Gbenga Daniel ya na makamancin wannan magana, ya ce akwai bukatar mulkin Najeriya ya koma yankin Kudu.

Tsohon gwamnan ya bukaci a sa batun kama-kama a tsarin mulki, ta yadda kujerar shugaban kasa za ta rika zagayawa tsakanin 'Yan Kudu da Arewa.

A ranar Litinin aka ji cewa Mataimakin Gwamnan Kuros Riba, Farfesa Ivara Ejemot Esu, ya ce ya sulale daga Jam’iyyar PDP, ya bi maigidansa, Ben Ayade.

Mataimakin Gwamnan ya fadi dalilinsa na barin PDP, Farfesa Esu ya ce an san Kuros Ribas da mutanen Kudu maso kudu da zama a Jam’iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel