Buhari ya dage taron majalisar zartarwa, yana makokin Attahiru da sauran jami'an soji
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dage taron majalisar zartarwa na tarayya da za a yi ranar Laraba zuwa makon gaba
- Ya kara da bada umarnin dage taron hukumar 'yan sanda da za'a yi a ranar Alhamis, zuwa Alhamis ta makon gaba
- Yayi hakan ne domin karrama marigayi Laftanal Janar Ibarhim Attahiru da sauran jami'ai 10 da suka rasu a hatsarin jirgin sama
Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bada umarnin dage taron majalisar zartarwa da ake yi a ranar Laraban kowanne mako.
Ya kara da mayar da taron majalisar 'yan sanda da za a yi a wannan Alhamis mai zuwa har zuwa ranar Alhamis ta makon gaba.
Kamar yadda sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya sanar, wannan dagewan an yi ta ne domin karrama tsohon shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami'ai goma da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin jirgin sama da suka yi a ranar Juma'a a Kaduna.
KU KARANTA: 2006: Yadda hatsarin jirgin sama ya ritsa da sojoji masu mukamin janar 10 a Binuwai
Takardar mai take 'Dage taron majalisar zartarwa ta tarayya da hukumar 'yan sanda'.
Ta ce, "Baya ga umarnin sauke tutocin kasar nan daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Mayun 2021, hutun ranar Litinin, 24 ga watan Mayu ga dukkan dakarun sojin kasar nan, shugaban kasa ya bada umarnin dage taron majalisar zartarwa na ranar Laraba 26 ga watan Mayu zuwa ranar Laraba 2 ga watan Yunin 2021.
"Hakazalika, taron hukumar 'yan sanda wanda za a yi a ranar Alhamis, 27 ga watan Mayu an dage shi zuwa ranar Alhamis, 3 ga watan Yunin 2021 domin karrama marigayi shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami'an soja 10 da suka rasu."
KU KARANTA: Mutum 2 sun fita da kumbo daga jirgin Janar Attahiru: Menene gaskiyar al'amarin?
A wani labari na daban, Dan majalisar wakilai, Abdulrazaq Namdaz, ya bada labarin yadda ya kusa shiga jirgin saman da yayi hatsari har ya kashe shugaban sojin kasa, Ibrahim Attahiru da wasu jami'ai 10.
Namdaz wanda ke shugabantar kwamitin al'amuran sojin kasa ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da Channels TV a ranar Lahadi, 23 ga watan Mayu.
Dan majalisar yace an gayyaceshi domin halartar yayen sojoji da za a yi a Zaria, jihar Kaduna. Ya ce da zai je kuwa babu shakka jirgin su Attahiru zai bi.
Asali: Legit.ng