Musulman Duniya Sun Yabawa Saudiyya Bisa Hannu a Dakatar da Rikici a Zirin Gaza
- Kungiyar kasashen Musulmi sun yabawa kasar Saudiyya bisa shiga tsakanin Isra'ila da Falasdinu
- Kamfanin dillacin labarain kasar Saudiyya ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar
- A baya Saudiyya ta yi kira ga Isra'ila cewa ta tsakaita wuta a kai wa yankin zirin Gaza hari
Kungiyar kasashen Musulmi (OIC) ta yaba wa gwamnatin Saudiyya kan kokarinta na tursasa Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare a Zirin Gaza, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito.
Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da mayakan Hamas ta ci gaba da aiki kwana uku a jere wanda ya kawo karshen rikicin kwanaki 11 da bangarorin biyu suka shafe suna yi.
SPA ya ce kungiyar OIC ta yaba wa Sarki Salman kan kalaman da ya yi a zantawarsa da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas cewa Saudiyya za ta ci gaba da bin matakan da suka dace domin matsin lamba ga Isra’ila ta dakatar da matakan da ta ke dauka da kuma hare-hare a birnin Kudus.
KU KARANTA: Jami'an Sojoji 4 da Ake Sa Ran Za Su Maye Gurbin Marigayi Janar Attahiru
OIC kuma ta yaba da kokarin mambobinta, musamman Masar da Jordan da kuma Qatar da suka taimaka wajen kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa.
A baya, ministocin harkokin wajen kasashen Masar da Saudiyya na kira da a tsagaita wuta nan take a fadan da ke tsakanin Isra’ila da Hamas a Zirin Gaza, AlArabiya ta ruwaito.
A wata sanarwa da aka fitar, ta ce Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan ya yi magana da Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry bisa rikicin da ke faruwa a Hamas da Isra'ila.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Uba da Dansa a Babban Birnin Tarayya Abuja
A wani labarin, A shekarar da ta gabata lokacin da Bill Gates ya bar shugabancin kamfanin Microsoft, ya ce aikin agaji ne ya sa ya yanke shawarar, amma sabon rahoto na danganta ficewar tashi da wani lamari da ya faru kusan shekaru 20 da suka gabata.
An ce yana karkashin bincike game da lamarin a shekarar 2019, yayin da kwamitin Microsoft ya nemi Gates ya sauka daga shugabancin kamfanin yayin da binciken ke gudana.
Maganar da ake zarginsa dashi ta kasance tare da wata injiniyar kamfanin Microsoft da ba a bayyana sunanta ba, wacce ta bayyana alakarta da shi a wata wasika. Lamarin ya bayyana ne yayin da Gates da matarsa, Melinda, ke fuskantar cuku-cukun saki.
Asali: Legit.ng