Shugabannin Fulani Da Tibi Sun Amince Da Tsagaita Wuta a Taraba

Shugabannin Fulani Da Tibi Sun Amince Da Tsagaita Wuta a Taraba

- Shugabannin Yan kabilar Fulani da Tibi a jihar Taraba sun amince da tsagaita wuta

- Kabilun biyu sun dauki lokaci mai tsawo suna rikici wadda ta janyo rasa rayyuka da muhalli

- Masu ruwa da tsaki daga bangarorin biyu ne suka kira taron suka cimma wasu yarjejeniya na kawo zaman lafiya

Shugabannin Fulani da Tibi a jihar Taraba sun amince da tsagaita wuta da nufin kawo karshen rikicin da ke tsakanin kabilun biyu da ya yi sanadin asarar rayuka a wasu sassar jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An tsagaita wutar ne bayan tattauanawa tsakanin masu ruwa da tsaki daga shugabannin ƙabilun biyu a Jalingo a jihar Taraba.

DUBA WANNAN: Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

Shugabannin Fulani Da Tibi Sun Amince Da Tsagaita Wuta a Taraba
Shugabannin Fulani Da Tibi Sun Amince Da Tsagaita Wuta a Taraba. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: UGC

Yayin tattaunawar ta masu ruwa da tsakin, an cimma yarjejeniya shida.

Yarjejeniyar da Alhaji Adamu Abacha, Sarkin Fulani Bali da Mr Zaki David Gbaa, Ter-Tiv Bali suka rattaba hannu a kai inda suka yarda a tsagaita wuta domin wadanda suka bar gidajensu saboda rikicin su koma.

Ƙabilan biyu sun kuma amince su yafe wa juna su zauna lafiya a matsayin ƴan uwa.

KU KARANTA: Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci

Sun kuma amince a kafa kwamiti ta wayar da kan mutane da za ta rika koyar da zaman lafiya a garuruwa.

Kazalika, sun amince kowa ya riƙa sa ido a unguwanni a kai ƙarar duk wani laifi wurin jami'an tsaro ko masu sarautar gargajiya.

Bayan haka, masu ruwa da tsakin sun shawarci mutanen ƙabilun biyu su saka ido kan wasu mutane da ke neman haɗa su faɗa ta kowanne hali.

Masu ruwa da tsakin sun kuma kafa kwamiti ta mutane 15 domin gano hanyar warware wannan rikicin dindindin.

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel