Cikakkun Bayanan Jami'an Soji 10 Da Suka Mutu a Hadarin Jirgin Sama Tare da Janar Attahiru

Cikakkun Bayanan Jami'an Soji 10 Da Suka Mutu a Hadarin Jirgin Sama Tare da Janar Attahiru

Ranar Juma'a, 21 ga watan Mayu, rana ce da Najeriya ba za ta taba mantawa ba, domin kuwa a ranar Najeriya ta rasa rayukan wasu jaruman sojojinta tare da shugabansu, Laftanal-Janar Ibrahim Attahiru a wani hadarin jirgin sama da auku a jihar Kaduna.

Janar Attahiru ya mutu tare da "sauran jami'ai 10", ciki har da mambobin sarrafa jirgin.

Ko da yake, kasancewarsa Shugaban Sojoji, bayanai daga fadar shugaban kasa, Sojojin Najeriya har ma da rahotannin kafofin yada labarai sun mai da hankali kan Attahiru yayin da aka bayyana ragowar wadanda suka mutu a matsayin "wasu 10".

Don girmamawa da tunawa dasu, wannan rahoto ya ba da takaitaccen bayanin dukkan jaruman da suka mutu, ciki har da Attahiru, wanda ya yi mutuwar "gwaraza a fafutukar samar da zaman lafiya a Najeriya," in ji rahotanni daga BBC Pidgin da shafin yanar gizon Sojojin Najeriya.

KU KARANTA: An Kame Wasu da Suka Yi Awon Gaba da Tirela Makare da Buhunnan Fulawa

Cikakkun Bayanan Jami'an Soji 10 Da Suka Mutu a Hadari Tare Janar Attahiru
Cikakkun Bayanan Jami'an Soji 10 Da Suka Mutu a Hadari Tare Janar Attahiru Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

1. Laftanar Janar Ibrahim Attahiru

An haifi Janar Attahiru ranar 10 ga watan Augustan 1966 a Doka, yankin karamar hukumar Kaduna ta Arewa, a jihar Kaduna.

Ya kammala karatunsa ne a Makaranta Tsaro ta Najeriya, da Kwamand na Sojoji da Kwalejin Ma’aikata da kuma Makarantar Sojoji ta Najeriya.

Janar Attahiru ya fara karbar horo ne a watan Janairun 1984 kuma an ba shi mukamin Laftanal na Biyu a Disamba 1986 a matsayin Jami'in Sojan kasa.

Ya rike mukamai da yawa akan ma'aikata, koyarwa da jagoranci yayin aikinsa na soja.

Marigayi COAS ya kasance kwamandan rundunar Operation LAFIA DOLE (mai yaki da ta'addanci da tayar da kayar bawa a Arewa maso Gabashin Najeriya).

Janar Attahiru ya kasance Mataimakin Daraktan Sakataren Soja na 2 a AHQ MS (A) kuma ya taba zama Daraktan Hulda da Jama’a na Soja sannan Kakakin rundunar Sojin Najeriya.

Janar din ya samu karramawa da kyaututtuka da yawa don yaba aikinshi.

Ya yi karatun digiri na biyu a fannin dabaru da nazarin manufofi daga Makarantar Tsaro ta Najeriya, Kimiyyar Harkokin Dan Adam da Ci Gaba daga Jami'ar Salford da ke Ingila da kuma babbar difloma a nazarin kasa da kasa daga Jami'ar Nairobi, Kenya.

Janar din ya yi aure cikin farin ciki kuma Allah ya albarkace shi da yara.

A ranar Talata, 26 ga watan Janairu, an nada Janar Attahiru Babban hafsan sojojin Najeriya.

2. Birgediya-Janar Mohammed Idris Abdulkadir

Birgediya-Janar M.I. An haifi Abdulkadir a ranar 19 ga Afrilu 1971 a jihar Kaduna.

Amma, ya fito ne daga jihar Neja a yankin arewa ta tsakiya. A cewar BBC Pidgin, ya zama Brig-Gen ne a ranar 17 ga watan Agusta 2017.

Har zuwa rasuwarsa, ya kasance Shugaban Ma’aikatan Laftana-Janar Attahiru Ibrahim.

Marigayi Brig-Gen Abdulkadir ya sami lambobin yabo da dama ciki har da lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya.

3. Birgediya-Janar Olatunji Olayinka

An haifi Birgediya-Janar Olatunji ne a ranar 13 ga Janairun 1970.

Marigayi babban jami'in sojan ya kasance daga Ikorodu a cikin jihar Legas. Ya kasance Provost Marshall na sojojin Najeriya sannan kuma ya samu lambar girmamawa daga Majalisar Dinkin Duniya.

4. Birgediya-Janar Abdulrahman Kuliya

An haife shi a ranar 2 ga watan Fabrairu, 1968, a Kano, Birgediya-Janar Abdulrahman Kuliya shi ne Mukaddashin Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Soja.

Ya hau mukamin Birgediya-Janar a ranar 10 ga Satumba, 2017.

Kuliya ya yi karatun digiri na farko a fannin ilimin lissafi sannan ya yi digiri na biyu a kan dabarun samar da albarkatun kasa da kuma dabaru da harkokin tsaro.

5. Manjo Nura Hamza

An haifi Manjo Nura Hamza a ranar 20 ga Nuwamba, 1979, a jihar Kano. Amma ya fito ne daga karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

Manjo Hamza ya halarci Jami’ar Bayero da ke Kano daga 1999 zuwa 2003, inda ya samu digiri na farko a kan ilimin tattalin arziki.

Ya kuma sami digiri na biyu a kan Tattalin Arzikin, Gudanar da Kasuwanci kuma ya kasance mamba a kungiyar Akawu ta Kasa na Najeriya (NAN).

Hamza ya zama Manjo a ranar 2 ga Disamba, 2015, kuma ya kasance a matsayin mukaddashin mataimakin daraktan kudi kafin rasuwarsa.

6. Manjo Lawal Aliyu Hayat

An haifeshi 11 ga Afrilu 1979, Manjo Lawal Aliyu Hayat ya fito daga karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.

Marigayi Manjo Hayat ya sami digiri na farko na Kimiyya a fannin Tattalin Arziki da Lissafin kudi kuma ya rike mukamai da dama.

Ya samu karin girma zuwa mukamin Manjo a ranar 27 ga Satumba, 2017.

7. Fl-Lt Ayodeji Olufade

An haifeshi ranar 19 ga Fabrairu, 1992, Laftanar Laftanar Alfred Ayodeji Olufade ya fito ne daga karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.

Olufade ya shiga rundunar sojan sama ta Najeriya ne a ranar 15 ga watan Agusta, 2009, kuma an kara masa girma zuwa Fl-Lt a ranar 15 ga watan Agusta, 2019. Ya samu digiri na farko na Kimiyyar lissafi n kdui a Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA).

Abokai da masu jaje sun nuna alhininsu game da rasuwar Olufade, wanda ya yi aure kimanin watanni uku da suka gabata.

Sa’o’i bayan tabbatar da mutuwarsa, hotuna da bidiyo daga bikin aurensa a watan Fabrairu sun fara yaduwa a kafafen sada zumunta.

Daya daga cikin abokansa ya ce ya yi matukar bakin ciki da labarin. A cewarsa, marigayin ya kan yi masa gori don fita daga gaurantaka. Ya kuma raba tattaunawar tasu a Tuwita.

8. Fl-LtTaiwo Olufemi Asaniyi

Dan asalin garin Ibadan a jihar Oyo, Olufemi Asaniyi an haifeshi a ranar 25 ga Fabrairu, 1992. Ya shiga rundunar Sojan Sama ta Najeriya ne a ranar 14 ga Agusta, 2010.

Asaniyi yana da digiri na farko na Kimiyyar Halitta daga Kwalejin Tsaro ta Najeriya. An ruwaito cewa ya yi aure kimanin watanni biyu da suka gabata.

Ya zama jami'in jirgin sama a ranar 12 ga Satumba 12, 2015, kafin a daga shi zuwa mukamin Flight-Lieutenant a ranar 14 ga Agusta, 2020.

Asaniyi, matukin jirgin sama Beechcraft 350 da ya lalace, an bayar da rahoton cewa yana shirin tafiya kan hanya tare da kaunar ransa a watan Oktoba kafin mutuwa ta zo ta kwankwasa masa.

A wani sakon da ya wallafa a shafin Tuwita ranar Asabar, kwana daya bayan faruwar lamarin, abokin Asaniyi, Adedeji Adeniyi ya bayyana cewa kwanan nan sun tattauna kan shirye-shiryen bikin marigayin mai zuwa nan da 'yan watanni.

A cewarsa, marigayin yana shirin aure, abin takaici, rai ya yi halinsa.

9. Sajan Umar Saidu

An haifeshi ranar 11 ga Disamba, 1985, Sajan Umar Saidu ya taso daga karamar hukumar Das ta jihar Bauchi.

Ya shiga a aikin Sojin Najeriya a 2006 kuma an tura shi zuwa rundunar 'yan sandan gidan sojoji daga baya.

Ya kasance yana aiki a bayyane ga marigayi Shugaban hafsan soja.

10. Sajan Adesina Isaiah

Sajan Adesina Opeyemi Isaiah an haife shi a watan Afrilun 1989 a jihar Kaduna.

An dauke shi aiki a rundunar Sojin sama ta Najeriya a ranar 2 ga Nuwamba, 2012. An ba shi mukamin kofur a ranar 2 ga Nuwamba, 2012 kuma ya zama sajan a watan Satumbar 2016.

11. Jami'i Oyedepo Matthew

An haifi Oyedepo Matthew a ranar 20 ga Maris, 1998, a jihar Osun. Ya shiga rundunar sojan sama ta Najeriya ne a matsayin shiga na gama-gari.

An bashi matsayin mai gyaran jirgin sama.

Bayan ya kammala horonsa na soja a cibiyar horas da sojoji a Kaduna, an tura shi zuwa kungiyar leken asiri ta 203, sa ido da kuma gano mutane a Yola, daga baya kuma aka tura shi Abuja kafin ya mutu.

KU KARANTA: Kada a Soke NYSC, a Horar da Matasa Kamar Sojoji Su Tunkari Matsalar Rashin Tsaro

A wani labarin, Misis Dolapo Osinbajo, matar Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan jami’an sojin da suka mutu a hadarin jirgin sama a ranar Juma’a 21 ga Mayu, a Kaduna.

Babban hafsan sojan, Ibrahim Attahiru, tare da wasu hafsoshin sojan 10 sun rasa rayukansu a hadarin jirgi.

Wata sanarwa da Ofishin Mataimakin Shugaban ya aike wa Legit.ng ta nuna cewa Misis Dolapo, nan da nan da jin labarin hadarin, ya sanya ta kai ziyarta ga iyalan jami’an soja da suka mutu, tare da jajanta musu da danginsu, tare da taya su jimamin babban rashin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel