Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo: Fadar Shugaban Kasa ta Magantu

Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo: Fadar Shugaban Kasa ta Magantu

- Wani rahoto dake bayyana cewa an ga Osinbajo a wani asibiti dake Legas ya sa 'yan Najeriya na tunanin bashi da lafiya

- Fadar shugaban kasa ta yi bayanin cewa shugaban kasan ya je asibitin ne domin duba ingancin lafiyarsa wanda yake yi duk shekara

- Bayan haka, Osinbajo ya koma Abuja inda ya cigaba da al'amuransa na yau da kullum kamar yadda ya saba

Fadar shugaban kasa tayi martani ga wani rahoto dake bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo bashi da lafiya kuma an gan shi a asibitin Reddington dake Legas a ranar Asabar, 22 ga watan Mayu.

Kamar yadda Sahara Reporters suka ruwaito, ganin Osinbajo a asibitin ya janyo tashin hankula da kuma tambayoyi daban-daban na dalilin zuwan mataimakin shugaban kasan asibitin.

KU KARANTA: Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Aisha Buhari ta kaiwa matar Janar Attahiru sun bayyana

Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo: Fadar Shugaban Kasa ta Magantu
Labarin Rashin Lafiyar Osinbajo: Fadar Shugaban Kasa ta Magantu. Hoto daga @akandeoj
Asali: Twitter

A yayin karin bayani, Sahara Reporters tace "Abinda yasa 'yan Najeriya suka damu da ganin mataimakin shugaban kasan a asibitin Reddington dake Legas shine ganin bai halarci jana'izar marigayi shugaban sojin kasa na Najeriya ba, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran jami'ai 10 wadanda suka yi hatsarin jirgin sama a Kaduna."

Amma kuma, Laolu Akande, babban mai bada shawara a fannin yada labarai, ya musanta rahoton a wata wallafa da yayi a Twitter wacce Legit.ng ta gani a ranar Litinin 24 ga watan Mayu.

Akasin tunanin jama'a da yadda Sahara Reporters ta ruwaito, Akande yace mataimakin shugaban kasa yaje asibitin Legas ne domin duba ingancin lafiyarsa kamar yadda yake yi duk shekara.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasan yace Osinbajo ya dawo Abuja da yammacin ranar Asabar, 22 ga watan Mayun 2021.

KU KARANTA: Da duminsa: Gawar Janar Attahiru da sojoji 6 ta isa Abuja daga Kaduna

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauke tutoci domin karrama marigayi Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasa da sauran sojoji 10 da suka rasa rayukansu yayin hatsarin jirgin sama na Kaduna.

Sojojin 11 suna cikin jirgin saman sojin Najeriya yayin da yayi hatsari kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na farar hula dake Kaduna a ranar Juma'a.

An shirya cewa Attahiru zai halarci taron yaye kananan sojoji a Kaduna a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel