Mutuwar Attahiru da sauran sojoji: Buhari yayi umarnin sauke tutoci na kwanaki 3

Mutuwar Attahiru da sauran sojoji: Buhari yayi umarnin sauke tutoci na kwanaki 3

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauke tutoci a dukkan gine-ginen gwamnati har da gidaje na kwana 3

- Yayi hakan ne domin karrama marigayi Janar Ibrahim Attahiru da sauran sojoji 10 da suka rasu a hatsarin jirgin sama

- Shugaban kasan ya kara da baiwa dukkan dakarun sojin kasar nan hutun ranar Litinin, 24 ga watan Mayu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin sauke tutoci domin karrama marigayi Ibrahim Attahiru, shugaban sojin kasa da sauran sojoji 10 da suka rasa rayukansu yayin hatsarin jirgin sama na Kaduna.

Sojojin 11 suna cikin jirgin saman sojin Najeriya yayin da yayi hatsari kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na farar hula dake Kaduna a ranar Juma'a.

An shirya cewa Attahiru zai halarci taron yaye kananan sojoji a Kaduna a ranar Asabar.

KU KARANTA: Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala

Mutuwar Attahiru da sauran sojoji: Buhari yayi umarnin sauke tutoci na kwanaki 3
Mutuwar Attahiru da sauran sojoji: Buhari yayi umarnin sauke tutoci na kwanaki 3. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

Kamar yadda takardar da aka fitar a ranar Lahadi daga Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, ta bayyana, an bukaci sauke tutoci a dukkan gine-ginen gwamnati da gidajenta na tsawon kwanaki uku.

"Domin karramawa tare da yaba ayyukan marigayi shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran sojojin da suka rasa ransu a hatsarin jirgin sama na ranar Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a rage tsawon tutoci a dukkan gine-ginen gwamnati da gidajenta daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Mayun 2021," takardar tace.

“Hakazalika, shugaban kasan ya amince da baiwa dukkan dakarun sojin kasar nan hutun ranar Litinin 24 ga watan Mayun 2021," Bashir Ahmad ya wallafa a Twitter.

KU KARANTA: Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matukar damuwa a kan hatsarin jirgin sama da yayi ajalin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana alhinin da shugaban kasan ya shiga.

"A yayin addu'a ga Ubangiji da ya gafartawa rayukan masu kishin kasan, shugaban kasan yace wannan babban rashi ne yayin da dakarun sojin kasar nan suka zage wurin ganin karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta," Shehu ya wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel