Da duminsa: Gawar Janar Attahiru da sojoji 6 ta isa Abuja daga Kaduna

Da duminsa: Gawar Janar Attahiru da sojoji 6 ta isa Abuja daga Kaduna

- Gawar marigayi COAS Attahiru tare da ta manyan sojoji shida ta isa garin Abuja daga Kaduna

- An kwashe gawawwakinsu daga inda hatsarin ya auku a Kaduna zuwa asibitin 44 na sojoji

- Shugaban sojojin kasa na Najeriya tare da tawagarsa sun rasu sakamakon hatsarin da suka tafka a jirgin sama

Gawar Janar Ibrahim Attahiru, marigayi shugaban sojin kasa da sauran sojojin da suka rasu sakamakon hatsarin jirgin sama a ranar Juma'a an daukesu daga Kaduna zuwa Abuja.

Mamatan sun rasa rayukansu ne sakamakon hatsarin da suka yi da yammacin ranar Juma'a a Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.

An kwashe gawawwakinsu daga inda suka yi hatsarin zuwa asibitin sojoji na 44 dake Kaduna daga nan aka mayar dasu Abuja.

KU KARANTA: Buhari ya fada jimami, ya nuna damuwarsa tare da ta'aziyyar Janar Attahiru

Da duminsa: Gawar Janar Attahiru da sojoji 6 ta isa Abuja daga Kaduna
Da duminsa: Gawar Janar Attahiru da sojoji 6 ta isa Abuja daga Kaduna
Asali: Original

KU KARANTA: Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala

Rundunar sojin kasan ta sanar da cewa za a yi jana'iza tare da birne sojojin da suka rasa rayukansu a ranar Asabar.

"An shirya jana'iza tare da birne shugaban sojin kasan Najeriya, Marigayi Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da sauran manya hafsin shida da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama a ranar Asabar, 22 ga watan Mayun 2021. Za a yi jana'izar a masallacin kasa da kuma cibiyar Kiristoci ta kasa a Abuja da karfe 1 na rana.

“Daga nan za a birne shugaban sojin kasan da manyan sojoji shida a makabartar kasa dake Abuja da karfe 1:30 na rana," Birgediya janar Mohammed Yerima, jami'in hulda da jama'a na sojin kasan Najeriya ya sanar a wata takarda.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matukar damuwa a kan hatsarin jirgin sama da yayi ajalin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana alhinin da shugaban kasan ya shiga.

"A yayin addu'a ga Ubangiji da ya gafartawa rayukan masu kishin kasan, shugaban kasan yace wannan babban rashi ne yayin da dakarun sojin kasar nan suka zage wurin ganin karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta," Shehu ya wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel