Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala

Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala

- Mazauna garin Maiduguri na jihar Borno sun fada farin ciki bayan jin labarin mutuwar Shekau

- Kamar yadda wani mazaunin garin ya sanar, sun dade suna addu'a kuma da Ramadan sun mika kukansu ga Allah

- Wani daga cikin mazauna yankin ya bukaci jami'an tsaro da su yi amfani da wannan damar wurin kakkabe 'yan ta'addan

Wasu mazauna garin Maiduguri, jihar Borno sun nuna jin dadinsu a kan rahotanni inda ake zargin cewa shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu.

Wasu mazauna Maiduguri da suka samu zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Juma'a, sun ce suna matukar farin ciki da labarin kuma suna fatan hakan ya zama gaskiya.

"Ina farinciki kamar yadda sauran suke a Borno a kan wannan zance. Ina fatan hakan ya zama cigaban da zai kawo karshen wannan al'amarin na ta'addanci," wani jami'in CJTF wanda ya bayyana sunansa da Lawan yace.

KU KARANTA: Birane 5 dake karkashin kasa, wurin da suke da labaransu masu cike da al'ajabi

Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala
Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kamfanin rarrabe wutar lantarki ya dawo da wutar jihar Kaduna

Wani dalibi mai suna Sadiq Ibrahim, ya ce labarin na nuna cewa wani abun arziki ne zai faru da jama'a da suka dinga fata ganin bayan ta'addanci.

"Muna ta addu'a shekara da shekaru kuma mun dinga addu'a ta musamman a Ramadan da ya gabata domin bukatar taimakon Allah. Hakan yana nuna cewa Allah ya karba addu'armu," Ibrahim yace.

Bala Musa direba ne da yace labarin babban abun farinciki ne ga jama'a wadanda ke fatan ganin karshen ta'addanci.

"Jama'a suna farin ciki da wannan cigaba kuma muna fatan gaskiya ne. Idan kun lura, duk inda kuka ga jama'a na hira, toh na murna ne kuma labarin mutuwar Shekau ne.

"Muna fatan jami'an tsaro zasu yi amfani da wannan damar wurin kawo karshen ta'addanci," Musa yace.

A wani labari na daban, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce nan babu dadewa za a shawo kan matsalar rashin tsaro kuma Najeriya zata samu zaman lafiya.

Ministan wanda ya samu wakilcin Lucky Irabor, shugaban ma'aikatan tsaro, ya sanar da hakan ne a wani taro kashi na 57 da aka yi a NAF Makurdi, babban birnin jihar Binuwai.

Ana samun jerin hare-hare a fadin kasar nan wanda ke kawo mutuwar jama'a, garkuwa da mutane da kuma kona gine-ginen gwamnati, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel