Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Atletico Madrid Ta Lashe Gasar Laliga

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Atletico Madrid Ta Lashe Gasar Laliga

- Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid ta samu nasarar lashe gasar Laliga ta wannan shekarar 2020/2021

- Ƙungiyar ta samu nasara ne bayan doke takwararta Real Valladolid a wasan ƙarshe da ci 2-1

- An kai ruwa rana tsakanin Atletico da abokiyar hamayyar ta Real Madrid dake biye da ita a kan teburin gasar ta Laliga

Ƙungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta lashe gasar laliga ta ƙasar sufaniya bayan samun nasara a wasanta na ƙarshe.

KARANTA ANAN: Wani Mutumi Yayi Yunƙurin Hallaka Limamim Ka'aba a Makkah

Tawagar ƙungiyar ta samu nasara ne a hannun ƙungiyar Real Valladolid wanda hakan yasa ta zama zakaraan gasar a wanna shekarar 2020/2021, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ɗan wasan ƙungiyar Valladolid Oscar Plano shine ya bude zura ƙwallo a raga inda ya jefa kwallo ta farko a wasan a minti na 18.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Atletico Madrid Ta Lashe Gasar Laliga
Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Atletico Madrid Ta Lashe Gasar Laliga Hoto: sports.ndtv.com
Asali: UGC

Sai dai tawagar Madrid ɗin ta maida martani inda ɗan wasanta Angel Correa ya rama mata kwallon da aka jefa mata a minti na 57, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

KARANTA ANAN: Amurka, Burtaniya Sun Bayyana Jimamin Su Kan Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru

Minti goma bayan wannan, tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar Barcelona, Luis Suarez, ya jefa kwallo a ragar Valladolid, wacce ta tabbatar da nasarar ƙungiyarsa ta Atletico.

A nata ɓangaren, abokiyar hamayyar ta da suke gari ɗaya, Real Madrid, ita ma ta samu nasarar doke Villareal da ci 2 - 1.

Duk da haka, tawagar koci, Diego Simeone ce ta samu nasarar lashe gasar da maki 86, kamar yadda the Nation ta ruwaito.

A wani labarin kuma IGP Yayi Magana Kan Barazanar Kai Hari Abuja da Plateau, Yace Mutane Su Kwantar da Hankalinsu

Sufetan yan sanda na ƙasa (IGP), Usman Baba, ya musanta zargin cewa hukumar tasan za'a kawo hari a Abuja da Plateau.

Sefetan ya bayyana haka ne a wani saƙo da kakakin hukumar yan sanda, Mr. Frank Mba, ya fitar yau a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel