Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Ta Goyi Bayan Gwamnonin Kudu Kan Hana Kiwo

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Ta Goyi Bayan Gwamnonin Kudu Kan Hana Kiwo

- Ƙungiyar miyetti Allah ta ƙasa ta nuna amincewarta kan matakin gwamnonin kudu na hana makiyaya kiwo a yankin

- Ɗaya daga cikin jigogin ƙungiyar na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, shine ya bayyana haka a taron manema labarai a Kaduna

- Sanatan yace ya kamata a zamanantar da kiwon shanu a nahiyar Afirca musamman a Najeriya.

Ƙungiyar fulani miyetti Allah (MACBAN), ta goyi bayan gwamnonin kudu kan matsayar su na hana fulani makiyaya kiwo a yankinsu, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Damƙa Sabbin Jiragen Yaƙi Uku Ga Rundunar Sojin Sama

Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Kaduna, jigon MACBAN na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, yace wannan matakin zai magance rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Ta Goyi Bayan Gwamnonin Kudu Kan Hana Kiwo
Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah Ta Goyi Bayan Gwamnonin Kudu Kan Hana Kiwo Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Sanatan yace kiwon shanu yakai tsawon sama da shekara 100 ana yinsa a nahiyar Africa ba tare da duba yadda shanun ke yawo ba ko samar musu da matsuguni.

KARANTA ANAN: Rundunar Soji Tayi Magana Kan Mutuwar Shugaban Boko Haram Sheƙau, Ta Faɗi Matakin da Zata Ɗauka

Yace: "A wancan lokacin akwai karancin fulani makiyaya, ƙarancin manoma da ƙarancin shanu shiyasa ba'a duba yiwuwar samar musu da wurin kiwo ba."

"Amma yanzun al'umma sun karu sannan akwai fasahohin noma da kiwo na zamani."

Sanata Jibrin, wanda shine Sarkin Fulanin Nasarawa, yace bisa damuwar da ake samu kan kiwon shanu a kafa a nahiyar Africa musamman Najeriya, akwai buƙatar a duba hanyoyin da za'a inganta shi.

A wani labarin kuma Ahmad Lawan Ya Caccaki Masu Sukar Majalisa, Ya Nemi Yan Najeriya Su Musu Adalci

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu ke sukar majalisa babtare da sanin ayyukanta ba.

Sanatan yace kamata yayi masu sukar majalisar dokoki su duba ayyukan da sukayi su soke su akansu ba wai da ra'ayi ba kawai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel