Zagin Buhari Sakarci Ne, Umahi Ya Ja Kunnen Matasan Kudu
- Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya je kunnen matasan yankin kudu maso gabas kan zagin Shugaba Buhari
- Umahi ya ce sakarci ne zagin Shugaban kasar, da shugabannin kudu maso gabas da ma wasu shugabannin da sunan gwagwarmaya
- Umahi ya ce matasan kudu su gabatar da kokensu sannan su basu watanni shida domin su tattauna da gwamnatin tarayya kan magance lamuran
Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi, a ranar Alhamis, ya fadawa fusatattun matasan kudu cewa gwamnonin kudu maso gabas za su mara musu baya idan ba a magance matsalar da suke fama da ita ba cikin watanni shida, The Punch ta ruwaito.
Umahi ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya ke halartar taron ministoci da tawagar sadarwa da fadar shugaban kasa ta shirya a Villa a Abuja.
DUBA WANNAN: Zamfara: Dole Manoma Su Fara Aiki a Gonakinmu Kafin Nasu, Dogo Giɗe da Black
Ya kuma bukaci matasan da ke fushi kan zargin wariya da ake nuna wa yankinsu su gabatar da kokensu.
Gwamnan ya bukaci su bawa gwamnonin watanni shida domin su tattauna da gwamnatin tarayya kan lamuran.
"Idan nan da watanni shida ba mu magance matsalolin da kuka gabatar ba, za mu mara muku baya a gwagwarmayar. Amma a yanzu, ba za mu goyi bayanku ba don ku zagi Shugaban kasa, shugabannin Kudu maso Gabas da wasu shugabannin. Wannan ba gwagwarmaya bane; wannan sakarci ne. Gwagwarmaya gwagwarmaya ce," kamar yadda ya fadi cikin wani sashi na jawabinsa.
Umahi ya ce akwai bukatar a yi amfani da hikima wurin magance batun wariya daga harkokin kasa.
KU KARANTA: Almundahanar Kuɗi: An Kama Wani Mutum Da Katin ATM 54 a Kano
Ya ce dole ne ta haifar da IPOB, ya kara da cewa gashi ta haifar da kungiyar Eastern Security Network.
"Kun ga yadda abin ke hayayyafa. Amma abin shine gwamnonin baya ba su magance matsalar yadda ya dace ba domin idan yaronka na kuka, ya kamata ka bincka dalilin sannan ka magance shi."
A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.
Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.
Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.
Asali: Legit.ng