Almundahanar Kuɗi: An Kama Wani Mutum Da Katin ATM 54 a Kano

Almundahanar Kuɗi: An Kama Wani Mutum Da Katin ATM 54 a Kano

- Jami'an hukumar Kwastam a jihar Kano sunyi nasarar damke wani mutum da katin ATM 54

- An kama mutumin, Abubakar Sale ne a lokacin da ya ke shirin hawa jirgin sama zuwa kasar Turkiyya

- Daga bisani, jami'an na hukumar Kwastam sun damƙa wanda ake zargin hannun hukumar EFCC don zurfafa bincike

Jami'an hukumar kula da shige da fice, Kwastam, sun kama wani da ake zargi da karkatar da kuɗaɗe, Abubakar Sale, sun gano katin ATM 54 tare da shi a Kano, The Punch ta ruwaito.

Kwantrola na hukumar Kwastam na Kano, SP Umar a ranar Laraba ya mika wanda ake zargin ga shugaban ofishin hukumar yaƙi da rashawa, EFCC, Mualledi Farouq Dogondaji domin a zurfafa bincike a kansa.

Almundahanar Kuɗi: An Kama Wani Mutum Da Katin ATM 54 a Kano
Almundahanar Kuɗi: An Kama Wani Mutum Da Katin ATM 54 a Kano. Hoto: @MobilePunch

DUBA WANNAN: Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP

A cewar sanarwar da EFCC ta fitar, jami'an na hukumar Kwastam sun damƙe wanda ake zargin ne a filin tashin jirage na Mallam Aminu Kano yayin da yake ƙoƙarin hawa jirgin Ethiopian Air domin zuwa Turkiyya.

Yayin da aka kama shi, an gano katin ATM 54 a hannunsa na bankuna daban-daban masu ɗauke da sunaye da dama.

Dogondaji ya yaba wa jami'an hukumar na Kwastam yayin da ya ke karɓar wanda ake zargin.

KU KARANTA: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

Kazalika, ya bada tabbacin cewa za a yi sahihin bincike kan lamarin, yana mai cewa hukumomin biyu za su cigaba da aiki tare.

A wani rahoton daban kun ji cewa abin baƙin ciki ya faru a unguwar Alanamu da ke ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a ranar Talata a lokacin da wani mutum Alhaji Taiye-Hassan Beki ya rasa ransa sakamakon gini da ya faɗo masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayin, Injiniyar lantarki mai yara huɗu yana fitsari ne a bayan gidansa lokacin ana ruwan sama sai wani sashi na ginin ya faɗo masa.

An dauki lokaci kafin a kai masa ɗauki domin ƴan uwansa ba su san abin da ya faru da shi ba a lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel