Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici

- Kasar Isra'ila da Hamas sun yanke shawarar tsagaita wuta tare da zama teburin sulhu

- Hakan na zuwa ne bayan bangarorin biyu sun kwashe kwanaki 11 suna kai wa juna hari

- A kalla Falasdinawa guda 232 ne suka rasu yayin da a bangaren Isra'ila mutane 12 ne suka mutu ciki har da yara

Ofishin Farai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Alhamis ta sanar da tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin da ta kwashe kwanaki 11 tana yi da kungiyar Hamas a zirin Gaza, Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar ta ce tawagar ofishinsa na bangaren tsaro ta amince da bukatar da sulhu da kasar Egypt za ta yi tsakanin bangarorin biyu.

Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici
Isra’ila da Hamas Sun Amince Da Tsagaita Wuta Bayan Kwana 11 Ana Rikici. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

Bangarorin biyu sun tattaunawa kan ainihin lokacin da tsagaita wutar zai fara aiki. Rahotanni da dama sun ce tsagaita wutar zai fara aiki ne misalin karfe 2 na daren Alhamis (Karfe 11 na daren Alhamis agogon GMT) awanni uku bayan amincewar tawagar.

A kalla Falasdinawa 232 ne suka rasu ciki har da yara 65 yayin rikicin da aka kwashe kwanaki 11 ana yi.

A bangaren Isra'ila, mutane 12 ne suka rasu guda biyu cikinsu yara.

Shugaban Amurka Joe Biden, a ranar Laraba ya tattauna kan abin da ke faruwa a zirin Gaza da Netanyahu, yana mai cewa yana fatan ganin an tsagaita wuta da nufin yin sulhu.

KU KARANTA: Bayan Komawa APC, Ayade Ya Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Tsaffin Takwarorinsa a PDP

Amma jim kadan bayan wayar da ya yi da Biden, Netanyahu ya ce zai cigaba da yi wa Gaza luguden wuta har sai Isra'ila ta cimma manufarta.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta yi kokarin sasanta bangarorin biyu amma hakarta bai cimma ruwa ba.

Tawagar ta Isra'ila cikin sanarwar ta ce sulhun da Egypt ke son a yi "zai amfani bangarorin biyu."

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel