Sojojin 'Yan ta'addan ISWAP 300 da aka yi wa horo a Libya suka yi sanadiyyar mutuwar Shekau
- Sojojin ISWAP akalla 300 suka shiga dajin Sambisa a ‘yan watannin nan
- Wadannan mayakan ne suka yi sanadiyyar mutuwar Abubakar Shekau
- Mayakan na ISWAP sun samu horo a kasashen Libya kafin su zo Najeriya
Sama da sojojin ta’adda 300 da su ka yi wa kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) ne su kayi sanadiyyar mutuwar Abubakar Shekau.
Jaridar Daily Trust a wani rahoto da ta fitar, ta ce wadannan mayaka da suka shiga dajin Sambisa, sun samu horo ne a Libya da wasu kasashen Duniya.
HumAngle da wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau bayan an yi kwana da kwanaki ana gwabzawa tsakaninsa da sojojin ISWAP.
KU KARANTA: Su wanene 'Yan ta'addan ISWAP?
Kamar yadda muka samu rahoto, ‘yan ta’adda ‘yan shekara 12 zuwa 30 ne suka yi gayya, suka shiga Sambisa, mafi yawansu, an kashe iyayensu a yaki.
Majiyar tace kungiyar ISWAP ta dauki hayar matasa suyi wannan aiki ne domin sun fi zafin nama. Mafi yawan sojojin ‘yan ta’adan fararen fata ne.
“An haifi wasunsu a lokacin da ake yakin, wasu kuma suna yara lokacin da iyayensu suka shiga kungiyar a 2002. Bayan iyayen sun mutu, sai suka gaje su.”
“A 2006 ne 'Yan Boko Haram suka rabu, wadanda su ka shiga tafkin Chadi a karkashin ISWAP sun fi sanin ta’addanci, domin an yi masu horo a kasar Libya.”
KU KARANTA: Sojoji sun yi magana a kan 'mutuwar' Abubakar Sheƙau
“Sauran sun tafi Siriya da Somalia, an kai su kasashe an ba su horo. Wadanda suka dawo tsakanin Maris zuwa Afrilun nan ne su ka bi ta kan Shekau a jeji.”
A wani kaulin, an ce daga cikin wadannan sojoji 300 har da likitoci, malaman lafiya, masana IT, da kwararru wajen harkar hada bam da masu gyaran na’urori.
Sojojin sun tare a garin Shuwaram da ke jihar Borno, bayan dawowarsu Najeriya. Daga cikinsu har da mata da suke aikin dafa abinci da masu rike da makamai.
A jiya ne rahotanni suka nuna Shekau ya yi mutuwar bakin wake ne bayan an tursasa masa ya mika wuya. Amma AFP ta ce ya harbe kansa ne da bindiga a kirji.
An ce bayan shugabannin ISWAP sun bukaci Shekau ya mika wuya, ya yi mubaya'a, sai ya nuna tamkar ya amince, daga baya sai ya tashi wani bam dake jikinsa.
Asali: Legit.ng