Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci

Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci

- Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da fitar da kudi Naira miliyan 155 domin siyan babura ga malaman addinun musulunci don da'awah

- Kwamishinan watsa labarai na jihar Sokoto, Alhaji Isah Galadanci ne ya sanar da hakan bayan taron kwamitin zartarwa na jihar

- Alhaji Isah Galadanci ya kuma ce kwamitin ta amince da ware Naira miliyan 196 domin aikin titi da shimfida kwalta a wasu yankunan jihar

Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kudi Naira miliyan 155 ga Ma'aikatan Harkokin Addinin Musulunci na jihar domin siya wa malamai babura a jihar domin su rika yin da'awah, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Alhaji Isah Galadanci ne ya bayyana hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron Kwamitin Zartarwa na jihar a ranar Alhamis 20 ga watan Mayun shekarar 2021.

DUBA WANNAN: 2023: Ɗan Shekara 35 Mai Neman Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi Taimakon Ahmed Musa

Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci
Tambuwal Ya Ware Wa Malamai N155m Don Da'awar Addinin Musulunci. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Har wa yau, kwamitin ta amince ta fitar da wani kudin fiye da Naira miliyan 196 domin gini da shimfida kwalta tagwayen titi mai tsawon kilomita biyar daga Achida-Tungar Malam-Lambar Kwali a ƙaramar hukumar Wurno na jihar.

KU KARANTA: Zamfara: Dole Manoma Su Fara Aiki a Gonakinmu Kafin Nasu, Dogo Giɗe da Black

Kwamishinan ya ƙara da cewa, "kwamitin ta kuma tattauna a kan shawarwarin da kwamitin da gwamnan ya kafa kan sauya kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari zuwa Jami'ar Ilimi; an kuma amince da kafa kwamitin aiwatarwa."

A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu sakamakon fashewar bututun iskar gas a cikin harabar Dakin Karatu na tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Abeokuta jihar Ogun a safiyar ranar Alhamis, rahoton Daily Trust.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar ta Ogun Gbenga Daniel ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel