Hotunan Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar muhimmin taro a kasar Faransa

Hotunan Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar muhimmin taro a kasar Faransa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki hudu a kasar Faransa

- Shugaban kasan ya halarci wani muhimmin taro ne na farfado da tattalin arzikin kasashen Afrika bayan korona

- Kamar yadda aka gano, shugaban kasan ya sauka a garin Abuja a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kasar Najeriya bayan tafiyar da yayi domin halartar muhimmin taro a birnin Paris na kasar Faransa, kamar yadda hadimin shugaban kasan Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Shugaban kasan ya iso kasar wurin karfe 5:15 na yammacin ranar Alhamis inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake garin Abuja.

KU KARANTA: An sheke mutum 1, wasu sun bace yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki Katsina

Hotunan Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar muhimmin taro a kasar Faransa
Hotunan Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar muhimmin taro a kasar Faransa. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

Idan zamu tuna, Buhari ya sauka garin Abuja a ranar Lahadi zuwa birnin Paris, inda ya kwashe kwanaki hudu domin halartar gagarumin taron farfado da tattalin arzikin Afrika bayan annobar Korona.

Taron ya mayar da hankali wurin duba tattalin arzikin Afrika bayan girgizashi da annobar Korona tayi, sannan ya samar da sassauci ballantana a fannin bashin da suke kan kasashen.

Taron wanda Shugaban kasa Emmanuel Macron na kasar Faransa ya karba bakunci, ya janyo manyan masu ruwa da tsaki na ma'aikatun kudi na duniya da wasu shugabannin gwamnatoci, wadanda suka zauna domin tattauna basussuka da kuma yadda kasashen Afrika zasu samu tallafi na kudi.

KU KARANTA: Nan babu dadewa zaman lafiya zai dawo Najeriya, Ministan tsaro

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce wadanda suka katse kasuwanci a jihar da sunan yajin aiki zasu dandana kudarsu.

A cikin kwanakin da suka gabata, mambobin kungiyar kwadago ta kasa da El-Rufai sun yi artabu a kan hukuncin gwamnatin jihar na sallamar sama da ma'aikata 4,000 a jihar.

A sakamakon hakan, kungiyar kwadago karkashin shugabancin Ayuba Wabba ta shiga yaji aikin kwanaki biyar wanda ta fara a ranar Litinin, The Cable ta ruwaito.

Wannan hukuncin bai yi wa El-Rufai dadi ba wanda ya bayyana cewa yana neman Wabba da sauran 'yan kungiyar kwadagon ruwa jallo a kan abinda ya kwatanta da zagon kasa ga tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel