An sheke mutum 1, wasu sun bace yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki Katsina

An sheke mutum 1, wasu sun bace yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki Katsina

- Miyagu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga garin Batsari dake jihar Katsina

- A take suka kashe wani Alhaji Iliya da ya koma garin a shekaru shida da suka gabata

- An nema mutum 27 an rasa duk da babu tabbacin cewa 'yan bindigan ne suka tisa keyarsu

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kai hari garin Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da wasu masu yawa.

Wani mazaunin Batsari wanda ya zanta da Daily Trust a waya yace Alhaji Iliya Bakon-Zabo, wanda ya koma Batsari a shekaru shida da suka gabata ne aka kashe yayin harin.

Ya ce kusan mutum 27 ne suka bace duk da har yanzu ba za a ce ko 'yan bindigan ne suka tisa keyarsu ba.

KU KARANTA: Duk da FG na ikirarin murkushe Boko Haram, ga jihohi 6 da ake zargin sun kutsa kai

An sheke mutum 1, wasu sun bace yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki Katsina
An sheke mutum 1, wasu sun bace yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki Katsina. Hoto daga @Vangaurdngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki

"Babu dadewa wata mata ta dawo. Don haka ba zamu iya cewa dukkan wadanda suka bace bane suke hannunsu. Amma a halin yanzu mun kirga babu mutum 27 da ba a san inda suke ba," yace.

Ya ce 'yan bindigan sun shiga Batsari ta yankin yammacin garin wurin karfe 12:10 na ranar Talata kuma sun dinga harbe-harbe babu kakkautawa.

Ya kara da cewa jami'an tsaro sun yi kokarin artabu da 'yan bindigan inda ya jaddada cewa ba don kokarinsu ba, da illar da zasu yi ta fi hakan.

Daily Trust ta tattaro cewa wannan ne karo na farko da 'yan bindiga suka shiga garin Batsari domin dukkan hare-harensu na baya sun kai ne kauyukan.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce 'yan bindigan da suka isa sun yi arba da 'yan sanda da sojoji.

A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da wani hari da miyagun 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka kashe mutum 8 tare da kone gine-gine a yankin.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda takardar tace, wadanda aka kashe a harin sun hada da: Samaila Gajere, Bawa Gajere, Bitrus Baba, Umaru Baba, Solomon Samaila, Sambo Kasuwa, Samaila Kasuwa da Gideon Bitrus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel