Nan babu dadewa zaman lafiya zai dawo Najeriya, Ministan tsaro

Nan babu dadewa zaman lafiya zai dawo Najeriya, Ministan tsaro

- Bashir Magashi, ministan tsaro yace zaman lafiya yana dab da dawowa kasar Najeriya

- Kamar yadda ya sanar, gwamnati ta shriya tsaf domin magance miyagun hare-haren da ake kaiwa jama'a

- Ministan yayi kira ga dakarun sojin Najerya da su kasance masu hadin kai domin tabbatar da cimma nasara

Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce nan babu dadewa za a shawo kan matsalar rashin tsaro kuma Najeriya zata samu zaman lafiya.

Ministan wanda ya samu wakilcin Lucky Irabor, shugaban ma'aikatan tsaro, ya sanar da hakan ne a wani taro kashi na 57 da aka yi a NAF Makurdi, babban birnin jihar Binuwai.

Ana samun jerin hare-hare a fadin kasar nan wanda ke kawo mutuwar jama'a, garkuwa da mutane da kuma kona gine-ginen gwamnati, The Cable ta ruwaito.

Amma a yayin jawabi ga sojojin, ministan yace rundunar sojin ta gama shiryawa tsaf domin kawo karshen matsalar tsaro.

KU KARANTA: Hotunan gidan Obafemi Awolowo sun bar jama'a baki bude cike da mamaki

Nan babu dadewa zaman lafiya zai dawo Najeriya, Ministan tsaro
Nan babu dadewa zaman lafiya zai dawo Najeriya, Ministan tsaro. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke mutum 8, sun kone coci da wasu gidaje a Kaduna

"Ina son tabbatar muku da cewa yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda ya kusa zuwa karshe. Za mu samu zaman lafiya a Najeriya. Kowanne sashi na kasar nan zai fuskanci zaman lafiya," yace.

"Sannanne abu ne idan aka ce rundunar sojin Najeriya na daga cikin jigon jami'an tsaro da ake bukata wurin tabbatar da daidaituwa.

"A don haka, ina kira gareku da ku yi iyakar kokarinku wurin tabbatar da cewa muna kan gaba wurin bada hadin kai yayin kawo karshen matsalar tsaron kasar nan.

“Na san muna da dakarun sojin da ke da karfin bamu kariya, yaki da kuma tabbatarwa da jama'a zaman lafiya. Dole ne ku kara jajricewa tare da hada kai domin fitar da mu kunya."

A wani labari na daban, duk da ikirarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na cewa ta ci galaba a kan 'yan ta'addan Boko Haram kuma ta kwace yankin arewa maso gabas, bayanan da ake samu daga wasu gwamnoni abun tsoro ne.

Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed a 2019 ya ce dakarun sojin kasar nan cike da nasara sun ci galaba kan mayakan Boko Haram. Ya ce Najeriya na fuskantar sabon salon rashin tsaro ne wanda ya zama ruwan dare dama duniya.

Sai dai a halin yanzu akwai jihohin da ke fama da hare-hare wanda ake zargin na 'yan ta'addan Boko Haram ne ke kaiwa, Premium Times ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel