Malami Ya Gargaɗi Gwmnonin Kudu a Kan Matakin Su Na Hana Makiyaya Kiwo

Malami Ya Gargaɗi Gwmnonin Kudu a Kan Matakin Su Na Hana Makiyaya Kiwo

- Antoni Janar na ƙasa (AGF), Abubakar Malami, ya gargaɗi gwamnonin kudu akan matakin da suke shirin zartarwa na hana kiwo a yankin su

- Malami yace Najeriya nada kundin tsarin mulkin da take tafiya a kanshi, kuma ya baiwa kowane ɗan Najeriya yancin yawo a faɗin ƙasa

- Yace matuƙar gwamnonin na son zartar da wannan dokar tasu, to wajibi ne su canza wannan yancin da ɗan Najeriya ke dashi

Antoni janar na ƙasa (AGF), Abubakar Malami, ya gargaɗi gwamnonin kudancin ƙasar nan kan matakin da suke shirin ɗauka na hana makiyaya kiwo a yankinsu.

KARANTA ANAN: Ahmad Lawan Ya Caccaki Masu Sukar Majalisa, Ya Nemi Yan Najeriya Su Musu Adalci

Da yake magana a cikin shirin channels tv 'Politics Today' ranar Laraba, Malami yace matakin gwamnonin bashi a cikin kundin tsarin mulki.

Malami Ya Gargaɗi Gwmnonin Kudu a Kan Matakin Su Na Hana Makiyaya Kiwo
Malami Ya Gargaɗi Gwmnonin Kudu a Kan Matakin Su Na Hana Makiyaya Kiwo Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

"Wannan abune da ya shafi yancin da kowa keda shi a cikin kundin tsarin mulki, shin zaku hana yan Najeriya yancin su ne?" Malami ya faɗa.

KARANATA ANAN: El-Rufai: Ƙarɓar Haraji Daga Yan Najeriya Ne Zai Iya Farfado da Tattalin Arziki Ba Kudin Man Fetur Ba

Malami ya roƙi gwamnonin kudu da su fara zuwa su nemi a gyara kundin tsarin mulki, a saka wannan dokar kafin su zartar da ita, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Malami Yace:"Idan ana magana akan yancin da ɗan Najeriya keda shi a cikin kundin tsarin mulki, to abinda yafi kyau shine kuje ku tabbatar anyi gyara a ciki, an saka muku abinda kukeso."

"Yancin ɗan Najeriya na yawo a ko ina cikin ƙasa yana ƙunshe a cikin kundin, idan kuna son kawo gyara a ciki sai ku tunkari majalisar dokoki, ku faɗa musu ya kamata a hana makiyaya kiwo, sai ku gani idan zasu goyi bayan ku a gyara kundin."

"Abu ne mai matuƙar hatsari wani gwamna a Najeriya yayi ƙoƙarin saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa bisa yancin da ya baiwa yan Najeriya."

A wani labarin kuma FG Ta Gayyaci Gwamnan Kaduna da Ayuba Waba, Ta Bayyana Ranar da Zasu Yi Taron Sulhu

Gwamnatin tarayya ta gayyaci gwamnatin Kaduna da shugabannin ƙungiyar ƙwadugo zuwa wajen taron sulhu a Abuja.

FG ta shirya taron ne a ƙoƙarin da take yi na samar da maslaha a tsakanin ɓangarorin biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262